Home Back

Jami’an tsaro ku gaggauta kawo ƙarshen faɗan Daba a faɗin Kano – Abba Gida-gida

dalafmkano.com 2024/7/3

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kawo ƙarshen faɗan Daba a faɗin jihar, tare da kira ga Alƙalai da su kasance masu zartar da hukunci ga duk wanda aka kama da tayar da hankalin al’umma domin ya zama darasi ga ƴan baya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan jawabin ne da safiyar yau Asabar, yayin taron majalisar zartarwa da gwamnati take yi a duk mako, domin aiwatar da aikace-aikacen gwamnati.

Gwamna Abba ya kuma yi kira ga Alƙalai da su zartar da tsattsauran hukunci akan duk wanda aka samu da laifin faɗan Daba.

A cewar sa, “Muna umartar dukkannin shugabannin ruƙo na ƙananan hukumomi 44, da su shiga lunguna da saƙo na jihar nan domin samar da ruwa musamman rijiyoyin Burtsate, “in ji shi”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta ce za tayi dukkannin mai yiyuwa wajen kawo ƙarshen faɗace faɗacen Daba a faɗin jihar kano.

People are also reading