Home Back

Liverpool na son daukar kocin Feyenoord Slot

bbc.com 2024/5/5
Arne Slot

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool na tattaunawa da Feyenoord kan batun daukar Arne Slot, domin maye gurbin Jurgen Klopp, wanda zai ajiye aikin a karshen kakar nan.

Klopp ya sanar cikin Janairu cewar zai ajiye akin, tun daga lokacin kungiyar Anfield ke ta neman wanda zai maye gurbinsa.

Kawo yanzu Liverpool na son daukar Slot, wanda ya ja ragamar Feyenoord a kakar 2022-23 ta lashe Eredivisie.

Feyenoord ta lashe Dutch Cup a bana, sannan tana ta biyu a babbar gasar tamaula ta Netherlands da ake kira Eredivisie.

An alakanta Slot da karbar aikin horar da Leeds United lokacin da ta kori Jesse Marsch a Fabrairun 2023.

Haka kuma ya musanta karbar aikin jan ragamar Tottenham a bara, wadda ta dauki Ange Postecoglou.

Mai shekara 45 yana da kunshin kwantiragin da zai kare da Feyenoord zuwa karshen kakar 2026.

Liverpool tana tattaunawa da Feyenoord, domin cimma matsaya, bayan da babu batun kudin da za a biya shi, idan yarjejeniyarsa bai kare ba.

Salon yadda yake horar da kwallon kafa ta kai hare-hare ya sa Liverpool ke son daukarsa, wanda aka ce Barcelona da Bayern Munich ma na son zawarcin kociyan.

Ya zama kocin Feyenoord a Disambar 2020, bayan da ya bar AZ Alkmaar, wadda ya taka rawar gani a kakarsa ta farko a aikin horar da tamaula.

Slot ya taka leda a Netherlands, wanda ya buga wasa sama da 100 a FC Zwolle da kuma NAC Breda.

Liverpool ta tuntubi Xabi Alonso tsohon dan wasan kungiyar Anfield, wanda ya sanar a cikin watan Maris cewar zai ci gaba da kociyan Bayer Leverkusen, wadda ta lashe Bundesliga na bana na farko a tarihi.

Haka kuma an alakanta mai horar da Sporting Lisbon, Ruben Amorim da cewar yana cikin wadanda Liverpool ke tuntuba.

People are also reading