Yan Sanda Sun Kama Mutane Sama da 100 Bisa Zargin Aikata Wasu Laifuka a Jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a ta ce jami’anta sun kama mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a cikin watan Maris.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X watau Twitter.
A sanarwar da ya fitar da yammacin Jumu'a, Kiyawa ya ce mutanen da aka kama sun hada da ƴan fashi da makami 15, masu garkuwa da mutane 4 da kuma wasu 10 da ake zargin dillalan kwayoyi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kazalika an kama wasu barayin motoci 4, barayin adaidaita sahu 3, barayin babura 7, ƴan damfara 2, barayi 20, da kuma 55 da ake zargin ƴan daba ne.
Kiyawa ya kuma bayyana cewa rundunar ta tarwatsa matsugunan masu garkuwa da yawa tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kwato kayan aikinsu.
Sauran kayan da ƴan sanda suka kwato sun hada da harsashi guda 15 na AK-47, harsashi guda 12 masu nauyin 7.62mm, bindigogin gida guda 24, motoci 7, Keke napep 3, babura 5, da wukake 28.
"Rundunar ‘yan sanda a tsakanin ranakun 1 zuwa 31 ga Maris, 2024, ta kara kaimi tare da aiwatar da tsare-tsare domin magance ‘yan daba a wasu wuraren da aka gano a cikin jihar musamman birni.
"Wasu daga cikin wadannan dabarun da aka yi amfani da su sun hada da daukar aikin 'yan sanda da dabara ta aiki, tare da kafa karin rukunin yaƙi da daba a Dorayi."
- Abdullahi Kiyawa.
A wani rahoton kuma Jami'an ƴan sanda da ƴan shi'a sun yi arangama ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 yayin da suka fito muzaharar ranar Quds a Kaduna.
Ƴan shi'ar sun fito da yawa a Kaduna amma ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa su saboda wasu daga cikin suna ɗauke da makamai.
Asali: Legit.ng