Home Back

Me ya kamata iyayen yaran da ake cin zali a makaranta su yi?

bbc.com 2024/5/4
..

Asalin hoton, getty images

Tun dai bayan da wani bidiyo ya fara waɗari a shafukan sada zumunta ranar Litinin na yadda wasu ɗalibai mata ke gaura wa wata ɗaliba mari, yayin da wani gungu kuma ke ɗaukar bidiyon, iyayen yara 'yan makaranta ke ta nuna damuwa dangane da al'amarin da neman yadda za su fahimci ana cin zalin 'ya'yan nasu.

Bisa kalaman da ke fitowa daga bidiyon, an fahimci cewa soyayya ce ta janyo rikicin, inda mai marin ke zargin wadda ake mari da ƙwace mata masoyi.

Bayan fitowar wannan bidiyo ne kuma sai wasu waɗanda suka fuskanci irin wannan cin zali su ma suka yi ta fito da bidiyo da hotunan cin zalin da suka fuskanta a makarantar.

To sai dai a wata sanarwa da makarantar mai suna Lead British School Abuja ta fitar, ta ce ta ga abin da ya faru kuma tana bincike domin tabbatar da ɗaukar matakin da ya dace.

To shin ko me ya kamata su kuma iyayen yaran da ake cin zali su yi?

'Jan ƴaƴa a jiki'

BBC ta tattauna da Dakta Hauwa Ɓaɓura masaniya kan harkar karatun ƙananan da lafiyar ƙwaƙwalwarsu kuma mai bai wa gwamnan jihar Jigawa shawara kan ilmi matakin farko, dangane da abin da ya kamata iyayen yara su yi domin gano ana cin zalin 'ya'yansu.

Dakta Hauwa ta ce matakin farko na gane abin da yaronka ko yarinyarki ke ciki a makaranta shi ne jan su a jiki.

"Idan dai har uwa ba za ta ja ɗanta ko ƴarta a jiki ba to da wuya iyaye su fuskanci halin da 'ya'yan nasu ke ciki. Ka ga ba za ki taɓa fahimtar lokacin da ƴarka ko ƴarki take cikin walwala ko akasin haka." In ji dakta Hauwa.

To sai dai kasancewar a wannan bidiyon da ya bayyana, ɗaliban da abin ya shafa a makarantar kwana su ke a saboda haka bai zama lallai mahaifa su fahimci halin da suke ciki ba.

Amma dakta Hauwa ta ce "ba haka ba ne saboda idan dai har iyaye suna jan 'ya'yansu a jiki to ai zamani ya ba su damar yin waya da catin sannan kuma ai ana zuwa ziyara akai-akai kenan yaran za su sanar da su idan dai suka nemi bayani dangane da halin da suke ciki." In ji dakta Hauwa.

Ɗaukar matakan shari'a

Dangane kuma da matakin da ya kamata mahaifi ya ɗauka bayan samun labarin cin zalin ɗa ko ƴarsa dakta Hauwa ta ce "duk abin da ya samu ɗanka ko ƴarka ka yi shiru to ka cuci wannan yaron ko yarinyar da ma sauran yaran da za su iya fuskantar irin wannan tsangwama a nan gaba.

Da zarar kun samu labari ko kuma kun fahimci hakan to a fara da ɗaukar matakan tuntuɓar makarantar idan kuma abin ya fi karfinsu sai a bi hanyoyin shari'a." A cewar dakta Hauwa.

Dakta Hauwa ta ƙara da gargaɗar makarantu cewa su ma da laifinsu sakamakon ko dai rashin bincike da sa ido ko kuma ɗauke kai daga abin da suke ganin bai taka kara ya karya ba.

"To amma idan iyaye suna zuwa su tunkari makarantun ko ma su ɗauki matakan shari'a to za ku ga makarantun suna ɗaukar matakan da suka dace. Sannan dole ne ita ma gwamnati ta saka idanu kan irin waɗannan makarantu." A ta bakin Dakta Hauwa.

Ire-iren cin zali a tsakanin yara

Emmanuel Paul Asan, ƙwararen likita kan tunanin ɗan adam da ke aiki a asibitin Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya lissafa ire-iren cin zali.

  • Cin zali na jiki: Wanna ya haɗa da duka da harbin dutse ko wani abu daban da tofawa wani yaro yawun baki da laƙawa wani yaro sata da ƙwacewa sauran yara kayansu da sauransu.
  • Zage-zage: Wannan ya haɗa da zagi mai cutarwa da zolaya da kiran wasu yaran da sunayen da bai dace ba saboda wani yanayi na halittarsu da wulaƙanci, da tsoratarwa, da kalaman nuna wariya har da na launin fata da cin zarafi da aibantawa, da cin zalin yaran da ke yawan shiru ko ba su cika magana ba da dai sauransu.
  • Cin zalin da jama'a suke yi: Wannan ya haɗa da harara domin tsoratarwa da cire wasu daga cikin wasu kungiyoyi, da tsegumi ko yaɗa jita-jita, da sanya wasu su zama kamar wawaye, da lalata mutuncin mutum da dai sauransu.
  • Cin zali a shafukan sada zumunta: A nan kuwa, za a ga yadda ake yaɗa abubuwan tsana idan wani ya ɗora hotonsa ko ya wallafa wani saƙo, da har zai saka mutum ya ji kamar duk an fi shi a duniya, wasu ma har suna kashe kansu kan irin waɗannan abubuwan, in ji likitan.
  • Cin zali na launin fata: Wannan ya haɗa da wulaƙanta mutane saboda ƙabilarsu ko kalar fatarsu ko al'adarsu da sauransu.
  • Cin zali kan addini: Wannan kuma ya haɗa da zaluntar mutane saboda asalin addininsu ko aƙidarsu in ji likitan.
  • Cin zali kan masu nakasa: Wannan shi ne kin yi hulɗa da wani ko gudun wani ko yi musu mugun nufi saboda suna da nakasa da sanya wani ya ji ba daɗi, ko yin barkwanci don cutar da wani saboda rashin lafiya ko nakasa.
  • Cin zali na jinsi: Wannan ya hada da yi wa wasu mutane mugun nufi, ko sanya musu rashin jin daɗi saboda jinsinsu ko yin barkwanci kan jinsin mutum ko taɓa mutum ba da izininsa ba ko kuma yaɗa jita-jita ta jima'i, in ji dakta Asan.

Illar da cin zali ke yi ga ƙwaƙwalwar yara

Dakta Emmanuel Paul Asan ya ce cin zali na shafar ƙwaƙwalwar yaro ta fanni daban-daban. Sun hada da

  • Haifar da ciwon ƙwaƙwalwa.
  • Mutum na iya kamuwa da hawan jini tun yana yaro har ya girma. Likitan ya ce cin zali na iya saka yaro ya kasance cikin rashin kwanciyar hankali da ƙunci da tsoro da bacin rai har girmansa.
  • Cin zalin yaro na iya jefa yaro cikin damuwa har idan ya girma ko da ace an daina zagin sa ko cin zalinsa.
  • "Yara na iya samun tunanin da bai kamata ba, kamar irin ba su da matsayi, sauran mutane sun fi su, suna ƙasƙantar da kansu, ko da sun san abu a aji, su kasa magana da sauransu.
  • Wasu yaran da aka zalunta suna girma da yunƙurin kashe kansu saboda tsananin cin zalin da aka yi musu.
  • Cin zali na iya jefa yaro cikin damuwa har idan ya girma ko da ace an daina zagin sa ko cin zalinsa.