Home Back

Ana Cikin Takaddamar Ganduje, 'Yan APC 1000 Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP a Kano

legit.ng 2024/5/18
  • Jam'iyyar All Progressives Congress ta samu koma baya bayan mambobinta mutum 1000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP
  • Masu sauya sheƙar sun samu tarba a gidan gwamnatin jihar inda aka karɓe su a matsayin sababbin ƴan jam'iyya mai mulki a jihar
  • Shugaban NNPP na jihar ya yi maraba da shigowar su jam'iyyar inda ya ba su tabbacin cewa za a dama da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sama da mambobin jam’iyyar APC 1,000 a jihar Kano sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP.

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo, shi ne ya karɓi masu sauya sheƙar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance a gidan gwamnati dake Kano, a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu.

'Yan APC sun koma NNPP a Kano
'Yan APC 1000 sun sauya sheka zuwa NNPP a Kano Hoto: Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Gwarzo ya yi wa kowane daga cikinsu ado da hular Kwankwasiyya, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba, ya fitar, ta ce waɗanda suka sauya sheka sun fito ne daga ƙananan hukumomin Shanono da Bagwai na jihar.

Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP tana fifita haɗin kai kuma za ta yi wa dukkan ƴaƴanta adalci.

Gwarzo ya jaddada ƙudirin gwamnatin na aiwatar da shirye-shiryen da za su amfana daukacin jihar Kano, ya kuma buƙaci a ci gaba da goyon bayan gwamnatinsu.

Meyasa suka bar APC zuwa NNPP?

Shugaban masu sauya sheƙar, Haruna Abbas, ya ce sun koma NNPP ne saboda halin shugabanci nagari da salon mulkin Gwamna Abba, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Ya nuna nadamarsa kan yadda suka kasance a jam'iyyar APC a baya, sannan ya yi alƙawarin yin tuƙuru da jam'iyyar NNPP domin ci gaban jihar Kano.

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi maraba da shigowar su jam'iyyar inda ya ba su tabbacin za a dama da su a cikin harkokin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

People are also reading