Home Back

A Karon Farko Cikin Kwanaki, Naira Ta Ci Karo da Matsala a Kasuwa, Ta Tashi da Kaso 1.38

legit.ng 2024/5/20
  • A karon farko tun ranar 20 ga watan Maris, darajar naira ta fado kasa kan N1, 169 a kasuwannin 'yan canji a Najeriya
  • A 'yan kwanakin nan darajar naira na kara tashi wanda ya saka tsammani a zukatan 'yan Najeriya kan saukowar farashin kaya
  • Hukumar kula da cinikayyar kudi (NAFEM) ta bayyana cewa faduwar naira ta samu da kaso 1.38 idan aka kwantanta da N1,159

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Darajar naira ta sake faduwa a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a kasuwannin 'yan canji.

A jiya ana siyar da dala kan N1,169 a kasuwanni idan aka kwatanta da ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu kan N1,159.

Hukumar kula da cinikayyar kudi ta NAFEM ta tabbatar da cewa naira ta fadi da kaso 1.38, cewar rahoton Tribune.

Wannan faduwar naira shi ne karon farko tun a ranar 20 ga watan Maris lokacin da dala ke N1,500.

Wannan na zuwa ne bayan Babban Bankin Najeriya, CBN ya musanta siyar da dala ga 'yan kasuwa kan N1,500.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading