Home Back

Hanyoyin kariya takwas daga faɗawa tarkon ɓata-gari a Adaidaita

bbc.com 2024/7/9
..

Asalin hoton, Getty Images

Wata matsalar da ke addabar biranen arewa maso yammacin Najeriya musamman Kano da Kaduna, ita ce ta faɗawa tarkon ɓata-gari da sunan direbobin Adaidaita ko kuma Keke Napep.

"Saboda tsabar rashin imani aka yankewa abokinmu ɗan yatsa a ƙoƙarinsu na ƙwace masa waya. Allah ya kyauta wannan bala'i." In ji wani wanda aka yankewa abokinsu yatsa a adaidaita a birnin Kano.

Mutane da dama sun fuskanci irin wannan hali sakamakon koƙarin ƙwace musu waya ko kuɗi ko kayan yari na mata da jakarsu ko ma ƙoƙarin sace su domin neman kuɗin fansa ko kuma su ba su ƙwaya domin su fita daga hayyacinsu yadda za su yi lalata da su.

Ɓata-gari dai kan yi basaja da sunan direbobin Keke Napep ko Adaidaita kamar yadda aka san shi, inda suke ɗibar fasinja wanda hakan ke ba su damar aiwatar da mugun nufinsu a kan jama'a.

Wannan ne ya sa BBC ta tuntuɓi Malam Yahuza Getso masanin harkar tsaro a Kano domin samar da shawarwarin da ya kamata jama'a su yi amfani da su a lokacin hawa keken. Kuma ya bayar da shawarwari guda takwas kamar haka:

(1) A guji adaidaita da sassafe ko bayan Magriba

Malama Yahuza Getso ya ce da farko dole ne mutane su fahimci cewa ba kowane lokaci ne ake hawan keke Napep ba.

"Dole ne a yi takatsantsan wajen hawa da sassafe ko kuma bayan Magariba saboda a wannan lokacin ne aka fi aikata ayyukan ɓata-gari sannan kuma waɗanda za su kawo ɗauki a lokacin sun yi ƙaranci idan ma har sun ankare kenan.

Saboda haka jama'a su guji hawa a wannan lokacin. Idan ma dole ne sai sun yi tafiya a lokacin za su iya amfani da wata hanyar ba wannan ba"

(2) Nazartar mutanen da ke cikin a adaidaita

Wani abu wanda ya zama wajibi ga duk mutumin da zai hau adaidaita ko kuma Keke Napep kamar yadda aka san shi a wasu wuraren "dole ne ya nazarci irin mutanen da ya tarar a ciki tun daga mai tuƙi har zuwa fasinjoji. Idan san samu ne ma a guji hawa adaidaita mai fasinjoji da yawa a ciki."

Mun sami yanayin da da matuƙin da fasinjojin duk bakinsu ɗaya ta yadda za su sanya fasinjan da suka ɗauka a tsakiya yadda ba shi da wani kataɓus." In ji Malam Yahuza.

(3) Ɗaukar hoton adaidaitan da za a shiga

Malam Yahuza ya bayar da shawarar cewa "idan adaidaita ya tsaya abin da ya kamata mutum ya yi ya ɗauki hotonsa sai ya aika dandalin whatsapp na iyali ko kuma ya tura wa iyalinsa ya faɗa musu ga abin da ya hau.

Sannan yana da kyau mutum ya buɗe alamar da ke nuna wurin da kake wato "location' domin iyalai su san inda mutum yake har zuwa ya kai ga gidansa."

(4) Sakaye abubuwan da ke ɗaukar ido

Wani da mutanen musamman fasinjoji ba sa fahimta shi ne sakaye duk wasu abubuwa masu muhimmanci kamar waya da jakar kuɗi kayan yari na mata kamar sarƙa da ƴan kunne masu tsada da dai sauran kayayyaki.

Sannan ka da mutum ya shiga adaidaita ya saki baki yana ta surutu musamman dangane da abubuwan da suka shafi kuɗi da sauran abubuwa masu daraja.

(5) Ka da ku hau wanda sai wani ya sauka kafin ku hau

Malam Yahuza ya ƙara da cewa ya kamata duk mai hawan adaidaita sahu ya kula cewa ka da mutum ya yarda wani fasinja ya sauka sannan kai kuma ka hau sai shi kuma ya koma daga baya.

"Ka ga kenan sun saka ka a tsakiya ta yadda duk abin da za su yi maka ba ka da wani kataɓus."

(6) Ka da ku yarda a sauya hanya

Wata matsala da mutanen da ke shiga adaidata sahu musamman da daddare shi ne yadda ana cikin tafiya sai kawai wani daga cikin fasinjoji ya ce a bi ta wata hanyar daban ba wadda ake tafiya a kai ba.

"A duk lokacin da wani fasinja ya ce haka to ka da ku yarda domin wataƙila suna son su shigar da ku sarƙaƙiya ne domin aiwatar da ayyukan ɓata-gari a kanku.

Ka da ku yarda. Idan ma ta kama ku yi kokawa ko hayaniyar da za ta saka hankalin jama'a ya koma kanku domin samun ɗauki". In ji Malam Getso.

(7) Amfani da kayan kariya

Domin kare kai masanin harkokin tsaron ya shawarci jama'a da su samu dan wani abu wanda zai iya taimaka musu idan suka shiga yanayi irin na ɓata-gari.

"Yana da kyau mutane su samu ɗan wani abun kare kai wanda hukumomin tsaro suka amince da a riƙe domin ceton kai kamar abin shokin mutumin da ke son cutar da kai.

Duk dai wani abun da jami'an tsaro ba za su zarge ka da riƙe shi domin ta'addanci ba." In ji Getso

..

Asalin hoton, Getty Images

(8) Amfani da lambobin waya na kar-ta-kwana

Daga ƙarshe Malam Yahuza Getso ya ce dole ne al'umma su rinƙa bai wa jami'an tsaro haɗin kai wajen ba su bayanan da za su kai ga kama masu irin wannan hali na ɓata-gari.

"Akwai lambobin waya na ko-ta-kwana da jami'an ’yan sanda da DSS da sauran masu rajin kawo ƙarshen ayyukan ɓata-gari ke bayarwa domin a kira su idan irin haka ta faru.

Ka da jama'a su yi shiru idan sun ga ana ƙoƙarin zaluntar su ko kuma waninsu domin hakan ne ke sa a bai wa mugaye mafaka".

People are also reading