Home Back

Za A Yi Gaggarumin Taron Bunkasa Noma A Legas

leadership.ng 2024/6/29

•Obasanjo Da Masana Aikin Gona Za Su Halarta

Aikin Gona

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo da sauran wasu masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma, za su halarci wani gagarumin taro a kan aikin noma da ake kira a turance ‘AgriConnect a 2024’.

Za a shirya wannan taro ne, don tattaunawa a kan yadda za a lalubo mafita wajen bunkasa fannin aikin noma a Nijeriya.

Kazalika, taron wanda za a gudanar a ranar 31 ga watan Mayun 2024, zai taimaka wajen hadaka tare da yin amfani da fasahar kere-kere, musamman don magance kalubalen da fannin aikin noma na wannan kasa ke fuskanta.

Har ila yau, taken taron shi ne, ‘Cike gibi ta hanyar yin hadaka tare da amfani da kirkire-kirkiren fasahar zamani, domin sama wa fannin aikin noma alkibla mai dorewa a nan gaba a fadin wannan kasa’.

Bugu da kari, taron na kwana guda, za a gudanar da shi ne a dakin taro na Cibiyar Landmarl event da ke Jihar Legas.

Kazalika, taron zai samu halartar masu ruwa da tsaki daga fannin kimiyya, ‘yan kasuwa a fannin aikin noma, cibiyoyin hada-hadar kudi da za su bayar da gudanunwarsu ga kanana da kuma manyan masu noma, domin samun riba da kuma yadda manoman za su rungumi wannan aiki na noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani tare da kuma ilimantar da su dabarun yin noma na zamani.

Mashiryin taron, Dakta Toyosi Obasanjo; a wata sanarwa da ya bai wa LEADERSHIP ya tabbatar da cewa, taron zai yi matukar taimakawa wajen cike gibin da ake da shi a wannan fanni na aikin noma da kuma kara karfafa hadaka da masu ruwa da tsaki daban-daban.

A cewarsa, daya daga cikin manufar taron ita ce, samar da dabarun da za su taimaka wajen magance kalubalen da fannin aikin noma na wannan kasa ke fuskanta tare kuma da samar da wadataccen abinci a fadin kasar baki-daya.

Ya sanar da cewa, Tsohon Shugaban Kasa; Cif Olusegun Obasanjo ne zai kasance shugaban wannan taro, wanda kuma sauran wadanda aka gayyata wadanda suka hada da mahukunta daga Bankin Masana’antu na Kasa, Bankin Union, Jakadan Faransa, USAID, IITA da kuma Microsoft, za su gabatar da kasidu.

People are also reading