Home Back

Yahaya Bello: An Bayyana Wurin da Tsohon Gwamna Ya Ɓoye Don Gudun Kamen EFCC

legit.ng 2024/7/2
  • Jigon PDP ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamna Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin jihar Kogi yana samun kariya daga Ahmed Ododo
  • Austin Okai, tsohon ɗan takarar majalisar tarayya ya faɗi haka ne yayin da EFCC ke ci gaba da koƙarin gurfanar da tsohon gwamnan a kotu
  • A watan Afrilu, 2024 hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo, inda ta roki al'umma su taimaka da bayanan wurin da ya ɓuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wani babban jigon jam'iyyar PDP, Austin Okai, ya fallasa wurin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ɓuya don kaucewa kamen EFCC.

Mista Okai ya bayyana cewa yanzu haka Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin Kogi da ke Lokoja ya ɓuya.

Yahaya Bello.
Jigon PDP ya ce Yahaya Bello na ɓoye a wani wuri a gidan gwamnatin jihar Kogi Hoto: Alhaji Yahaya Bello Asali: Facebook

Tribune Nigeria ta tattaro cewa a watan Afrilun da ya gabata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan gazawar da tsohon gwamnan ya yi na kawo kansa gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

EFCC ta buƙaci duk wanda ke da masaniyar da wurin da Bello ya ɓuya, ya gaggauta kai rahoto ga ofishin hukumar ko kuma caji ofis mafi kusa.

Hukumar EFCC na zargin Yahaya Bello da halasta kuɗin haram da suka kai N80bn a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar Kogi, rahoton Daily Post.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, jigon PDP ya yi zargin cewa Gwamna Ododo ya taka rawa har Bello ya gujewa EFCC ta hanyar dauke shi daga gidansa na Abuja.

Autin Okai tsohon ɗan takarar kujerar majalisar tarayya a inuwar PDP ya ƙara da cewa:

"Ana kyautata zaton Yahaya Bello yana boye a gidan gwamnatin jihar Kogi, inda gwamnan ke ba shi kariya.
"Maganar gaskiya ita ce, ana zargin Yahaya Bello ne ke bai wa Gwamna Ahmed Usman Ododo daga wani buyayyar wuri a gidan gwamnatin."

Kano: Falana ya soki hukuncin kotu

A wani rahoton kuma Femi Falana ya soki hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a shari'ar sarautar Kano, ya ce akwai ruɗani.

Fitaccen lauyan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam ya ce hukuncin yana da ɗaure kai domin kotun koli ta hana kotunan tarayya tsoma baki a sha'anin sarauta.

Asali: Legit.ng

People are also reading