Home Back

Rundunar Sojojin Najeriya ƙasar nan ta ke wa aiki, ba ƙungiyar sa-kai ta wata ƙabila ba ce – Hukumar Sojoji

premiumtimesng.com 2024/5/19
BIKIN KAMMALA HORAS DA KURATAN SOJOJI: Ba sauran hutu sai mun kakkabe matsalar tsaro –  Janar Ali Keffi

Hukumar Sojojin Najeriya ta ƙaryata tare da nesanta zargin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yi mata, cewa ta na ƙoƙarin hukunta wasu sojoji ‘yan kudu da suka yi laifi, su kuma sojojin Arewa an ƙyale su ba a maganar hukunta su.

Zargin dai ya biyo bayan shari’ar da aka fara yi wa wasu sojoji a kotun soja da ke cikin Barikin Dibijin na 82 da ke Enugu.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Sojan Najeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a Abuja, ya ce Sojojin Najeriya sun ƙunshi kowace ƙabilar ƙasar nan, ba sojojin sari-ka-noƙe ba ne na wata ƙabila.

Ya ce rahoton da aka buga wai ya nuna wasu sojojin da aka gurfanar a kotun sojoji ta cikin Barikin Sojojin Enugu, sun nuna damuwar su.

Ya ce rahoton maras kan-gado ne, kawai an ƙirƙire shi don a haifar da rashin fahimta da ƙiyayya a tsakanin Sojojin Najeriya.

Ya ce rahoton ƙarya ce tsagwaron ta, kuma babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan.

Ya ce waɗanda suka ƙirƙiri rahoton su na ƙoƙarin haddasa ƙiyayya da rashin haɗin kai ne a tsakanin sojojin Najeriya da kuma kitsa ƙabilanci da addinanci.

Ya ce Shugaban Kotun ɗan Arewa ne, yayin da alƙalin Kotun ɗan Kudu ne. Sannan ya ce kashi 60 bisa 100 na mambobin kotun ‘yan Kudu ne.

“Sannan kuma ba addinanci ko ƙabilanci ake amfani da shi wajen hukunci ba. Haka kuma ba mutum ɗaya ne ke yanke hukunci ba. Duk hukuncin da za a yanke, baki ɗaya ɗayan su ne ke cimma matsaya guda.”

People are also reading