Home Back

Sai mutane sun bada gudunmawa za’a kawo ƙarshen matsalar tsaro a Ƙasa- Gamayyar ƙungiyoyin Arewa

dalafmkano.com 2024/6/29

Gamayyar kungiyoyin Arewacin kasar nan, wato Coalition of Northern Groups CNG, ta ce matukar ana so a kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Arewacin kasar nan sai kowa ya ba da gudunmawar sa a harkar tsaron.

Jami’in gudanarwar gamayyar kungiyoyin na kasa kwamared Jamilu Aliyu Chiranchi ne ya bayyyana hakan a yayin taron manema labarai da ta gudanar yau Juma’a a nan Kano.

Ya kuma ce, taron na su ya biyo bayan zaman da su ka yi da masu sana’ar finanan Hausa da masu shirya wasan da kuma masu amfani da kafafan sadarwa na zamani.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, gamayyar kungiyoyin na Arewa sun ce nan gaba kadan za su zauna da ‘yan jarida da kuma mamallaka gidajen jaridun dangane da yadda za a shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin na Arewacin kasar nan.

People are also reading