Home Back

Masana Sun Fallasa Yadda Gwamnatin Tarayya da Dawo da Tallafin Man Fetur a Boye

legit.ng 2024/7/1
  • Bincike ya nuna an samu tashin farashin kudin jigilar man fetur daga ƙasashen ketare a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024
  • Hakan yana nuna cewa gwamnatin tarayya tana saka tallafi a harkar man fetur saboda saukaka farashinsa a gidajen mai
  • Har ila yau sun yi hasashen hauhawar farashin a watan Yunin da muke ciki ganin abubuwan da suka saka tsadar man sun karu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Binciken masana ya nuna an samu tashin farashin kudin jigilar man fetur daga ƙasashen ketare zuwa Najeriya da kashi 46.8%.

An jingina dalilin tashin farashin ga tashin dalar Amurka da ake amfani wajen hada-hadar shigo da man fetur gida Najeriya.

Man fetur
Kudin shigo da man fetur ya karu, gwamnati ta dawo da tallafi a boye. Hoto: Bloomberg/Contributor Asali: Getty Images

Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ya nuna cewa har yanzu gwamnatin tarayya na saka tallafi a harkar domin kaucewa tashin farashin mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin litar fetur daga ketare zuwa Najeriya

Binciken masana ya tabbatar da cewa kowace litar mai na zuwa gida Najeriya daga ketare kan N1,052.39.

Bayan haka masu hada-hadar man suna biyan kudin haraji, kudin ajiyar kaya da sauran kudin jigila daga jiha zuwa jiha.

Masu harkar man fetur sun koka

Saboda yadda shigo da kayan ya kara kudi masu harkar mai sun bukaci gwamnatin tarayya kar ta kayyade farashin mai.

Sun ce kayyade farashin zai iya jawo asara ga 'yan kasuwa ta yadda ba za su rika samun riba yadda ya kamata ba.

Kididdigar da NBS ta fitar

Saboda tashin farashin shigo da man fetur ne cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce an samu tashin farashin man fetur da kashi 176.02%.

Cibiyar ta ce hakan yasa aka samu karin farashin man fetur zuwa N701.24 a watan Mayun da ya wuce wanda a shekarar 2023 bai wuce 254.06 ba.

Masana sun bayyana cewa sanya tallafi da gwamnatin tarayya ta yi shi ya hana tashin farashin mai sosai a Najeriya.

Kuma har ila yau wasu na amfani da damar wajen safarar man fetur zuwa kasashen ketare tare da cewa farashin zai iya karuwa nan gaba kadan.

Farashin mai ya tashi a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuna cewa ana samun tashin farashin man fetur a wasu gidajen mai da ke yankunan jihar Lagos.

Wani dan kasuwa ya bayyana cewa suna sayan mai a hannun 'yan kasuwa ne saboda haka suka daga farashin domin samun na goro.

Asali: Legit.ng

People are also reading