Home Back

A Inter Miami Zan Yi Ritaya – Messi

leadership.ng 3 days ago
A Inter Miami Zan Yi Ritaya – Messi

Tsohon dan wasan Barcelona da PSG, Lionel Messi ya yanke shawarar yin ritaya daga kwallon kafa a Inter Miami – sai dai kawo yanzu bai tsara lokacin da zai bayyana yin ritayar ta sa ba. 

Dan wasan mai shekara 36, mai kyautar Ballon d’Or takwas, ya koma buga gasar kwallon kafa ta Amurka a kakar wasa ta 2022/23, bayan da kwantiraginsa ya kare a Paris St-Germain.

Kyaftin din na tawagar Argentina ya nuna kansa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda ya lashe gasar cin Kofin Zakarun Turai guda hudu da La Liga 10 a kungiyar da ke Sifaniya. Wanda ya dauki kofin duniya a 2022 da Argentina a Katar a 2022, yana da sauran kunshin yarjejeniya da za ta kare a Inter Miami zuwa karshen kakar wasa ta shekarar 2025.

Kawo yanzu dai dan wasa Messi yana wasa kan ganiya ba za ka ce zai yi ritaya kwanan nan ba, wanda ya ci kwallo 12 da bayar da 13 aka zura a raga a wasa 12 a gasar ta Amurka.

Kuma kawo yanzu yana wakiltar kasar Argentina a gasar cin kofin kudancin Amurka wato Copa America, da a yanzu ake bugawa a kasar Amurka a bana, wadda ita take da kofin da ta dauka a 2021 a Brazil.

People are also reading