Home Back

CBN ya umarci bankuna su ƙara yawan jarin hada-hadar bankunan su nan da watanni 24

premiumtimesng.com 2024/5/13
Yadda zan tsayar da taɓarɓarewar darajar naira – Cardoso, sabon Gwamnan CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan Najeriya cewa kowane ya ƙara yawan jarin kuɗaɗen hada-hadar sa.

An buƙaci bankunan cewa kowane ya tabbatar da ya ƙara aƙalla adadin da aka umarce shi ya ƙara, nan zuwa watanni 24 masu zuwa.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta Riƙo ta CBN, Hakama Ali ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ana buƙatar ƙarfin jarin duk wani banki mai rassan hada-hada a ƙasashen waje ya kasance Naira biliyan 500, yayin da bankunan cikin ƙasa kawai ya kasance ƙarfin na da ƙarfin ƙarin Naira biliyan 200.

CBN ya ce ƙananan bankuna da ke yankunan ƙasar nan daban-daban kuma, na su ƙarfin jarin kada ya gaza Naira biliyan 50.

CBN ya ce an umarci kowane banki ya cika waɗannan sharuɗɗa nan da tsawon watanni 24 daga ranar 1 ga Afrilu. Wato kada wani banki ya wuce ranar 31 Ga Maris, 2026 bai cika sharuɗɗan ba.

People are also reading