Home Back

Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano

leadership.ng 2024/5/9
Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano

A wani mummunan lamari da ya faru a ranar Juma’a, 26 ga Afrilu, 2024, wasu magina da ba a tantance adadinsu ba sun makale a lokacin da wani gini ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Rahotannin farko na cewa, akalla mutane 11 ne suka makale a karkashin baraguzan ginin da ake kan ginawa. Jami’an bayar da agajin gaggawa na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) da hukumar kashe gobara ta jihar na aikin ceto wadanda suka makale.

An samu nasarar ceto mutane biyu kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Har yanzu dai ba a san musabbabin rugujewar ginin ba ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

People are also reading