Home Back

Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara

leadership.ng 2024/6/26
Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara

Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci ta Tarayya, ta shirya tsaf; domin fara rabon buhunan takin zamani miliyan 2.15, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ba ta kauta.

Wasu masana a fannin aikin noma a kasar nan; sun bayar da shawarar cewa, duba da yadda aka fara samun ruwan sama a wasu sassan yankunan kasar nan, ya kamata a fara raba wa manoma takin a kan lokaci, musamman domin samar da wadataccen abinci.

Sai dai, wata majiya a ma’aikatar ta bayyana cewa, an samu jinkirin rabar da takin zamanin ne; sakamakon gudanar da binciken da aka yi na zargin cewa, takin ya lalace.

A cewar majiyar, “Babban Bankin CBN, ba wani sabon takin zamanin zai sayo ba, sauran wanda Tsohon Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele ya gaza rabawa ne a karkashin shirin  aikin noma na babban bankin, wato ‘Anchor Borrower Programme’.”

Har ila yau, majiyar ta kara da cewa; wannan taki, bankin CBN ne ya mika wa ma’aiktar aikin noma, amma akwai wasu abubuwa da ma’aikatar ke bukatar tantacewa kafin ta fara rabar da takin.

Haka kazalika, akwai wani zargi da ake yi na cewa, tuni takin ya jima da lalacewa.

Koda-yake, an kuma ruwaito cewa; Daraktan sashen kula da ayyukan samar da kayan aiki noma na ma’aikatar, Abana Waziri Abba, ya karyata batun zargin lalacewar takin zamanin.

Sai dai kuma, ya aminta da cewa; sashen ya dauki samfurin takin, don gudanar da gwaji a dakunan gwaje-gwajen da ake da su a Jihar Kaduna da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma Jami’ar  Bayero da ke Kano, don tabbatar da ingancinsa; domin wannan sashe ne ke da alhakin tabbatar da ingancin kowane irin taki a fadin kasar nan.

A cewarsa, sakamakon binciken ya nuna cewa, takin na da inganci; sannan kuma za a iya sayar wa da manoma, inda ya sanar da cewa, sai dai kawai wasu ‘yan matsaloli da ba za a rasa ba a kan takin.

Sai dai, bai yi bayani dalla-dalla kan yadda za a yi rabon takin ga manoman da ke fadin Nijeriya ba.

Kazalika, yawan takin ya kai kimanin buhu miliyan 2.15, sannan kowane nauyin buhu daya ya kai nauyin kilo 50.

Sa’annan, nau’in takin ya hada da NPK tan 27,250; 20-10-10 da wani tan 27,110.00 na NPK 27-13-13 da tan 18,904.55 na NPK 15-15-15  378,091 da tan  31,772.18 na nau’in UREA 635,444 da kuma tan 2,500 na nau’in  SSP 50,000.

Jimillar wadannan nau’ikan baki-daya ya kai yawan buhu 2,150,735, wadanda awonsu ya kai kimanin tan 107,536.73.

People are also reading