Home Back

"Kanku Ake Ji": El Rufai Ya Yi Zazzafan Martani Kan Zargin Badaƙala a Kaduna, Ya Bugi Kirji

legit.ng 2024/7/5
  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya magantu kan binciken da kwamitin Majalisar jihar ta gudanar game da gwamnatinsa
  • El-Rufai ya ce wannan mataki na kwamitin Majalisar kawai bita da kullin siyasa ne amma ya gudanar da gwamnatinsa cikin gaskiya
  • Hakan na zuwa ne bayan kwamitin ya bukaci hukumar yaki da cin hanci ta cafke El-Rufai kan zargin badakala lokacin mulkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi martani kan zargin badakala a gwamnatinsa.

El-Rufai ya yi fatali da rahoton Majalisar jihar kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Muyiwa Adekeye a yau Laraba 5 ga watan Yuni, cewar Channels TV.

Ya ce wannan matakin Majalisar kawai bita da kullin siyasa ne inda ya tabbatar da cewa ya jagoranci gwamnati mai tsafta yayin mulkinsa.

"Nasiru El-Rufai yana alfahari da ayyukan alheri da ya gudanar a jihar Kaduna yayin da ya ke gwamna."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mafi yawan wadanda suka yi gwamnati da El-Rufai sun gurfana a gaban kwamitin wanda ke nuna kwarin guiwa kan irin gwamnatin daya gudanar."
"El-Rufai yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa ya gudanar da mulki cikin gaskiya da bin doka tare da taimakon mukarrabansa kwararru."
"Ya bukaci a yi fatali da wannan bincike na son rai da kuma bita da kullin siyasa da ake yi."

- Muyiwa Adekeye

Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar ya bukaci a hukunta El-Rufai da mukarrabansa saboda zargin badakala a gwamnatinsa.

Har ila yau, kwamitin ya bukaci dakatar da kwamishinan kudi a Kaduna, Shizer Badda wanda ya rike mukami a gwamnatin Nasir El-Rufai.

Karin bayani na tafe ...

Asali: Legit.ng

People are also reading