"Kanku Ake Ji": El Rufai Ya Yi Zazzafan Martani Kan Zargin Badaƙala a Kaduna, Ya Bugi Kirji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi martani kan zargin badakala a gwamnatinsa.
El-Rufai ya yi fatali da rahoton Majalisar jihar kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Muyiwa Adekeye a yau Laraba 5 ga watan Yuni, cewar Channels TV.
Ya ce wannan matakin Majalisar kawai bita da kullin siyasa ne inda ya tabbatar da cewa ya jagoranci gwamnati mai tsafta yayin mulkinsa.
"Nasiru El-Rufai yana alfahari da ayyukan alheri da ya gudanar a jihar Kaduna yayin da ya ke gwamna."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mafi yawan wadanda suka yi gwamnati da El-Rufai sun gurfana a gaban kwamitin wanda ke nuna kwarin guiwa kan irin gwamnatin daya gudanar."
"El-Rufai yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa ya gudanar da mulki cikin gaskiya da bin doka tare da taimakon mukarrabansa kwararru."
"Ya bukaci a yi fatali da wannan bincike na son rai da kuma bita da kullin siyasa da ake yi."
- Muyiwa Adekeye
Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar ya bukaci a hukunta El-Rufai da mukarrabansa saboda zargin badakala a gwamnatinsa.
Har ila yau, kwamitin ya bukaci dakatar da kwamishinan kudi a Kaduna, Shizer Badda wanda ya rike mukami a gwamnatin Nasir El-Rufai.
Karin bayani na tafe ...
Asali: Legit.ng