Home Back

UNICEF ta tallafa wa Jigawa da katan 12,400 na abinci mai gina jiki, domin raba wa ƙananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki

premiumtimesng.com 2024/8/25
UNICEF ta tallafa wa Jigawa da katan 12,400 na abinci mai gina jiki, domin raba wa ƙananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki

Gwamnatin Jihar Jigawa ta karɓi tallafin katan 12,400 na Haɗɗaɗɗen Abincin Yara Mai Gina Jiki (RUTF), wanda za ta raba wa ƙananan yaran da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Tallafin na abincin ya kai na aƙalla Naira miliyan 500, wanda aka samar ƙarƙashin yarjejeniyar ‘Matching Fund’, tsakanin Gwamnatin Jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Tallafin Inganta Lafiyar Ƙananan Yara ta UNICEF.

Daraktan Unicef a Najeriya, Christian Munduate, ta miƙa wa gwamnatin Jigawa kayan tallafin, domin fara rabawa.

Wannan ziyara da wakiltar UNICEF ta kai Jigawa ta kuma aza harsashen aikin farfaɗo da Cibiyoyin Kula da Lafiya 30 a yankuna 30 na faɗin cikin jihar.

Wannan shiri wani hoɓɓasa ne domin magance ƙalubalen matsalar abinci mai gina jiki ga ƙananan yara a jihar.

Matsalolin da ake son a shawo kan su, sun haɗa da a tabbatar samuwar abinci mai gina jiki ga ƙananan yara.

UNICEF ta ce a shirye ta ke fiye da kowane lokaci a yanzu wajen tabbatar da cewa ta yi duk wani abin da ya zama tilas wajen inganta lafiyar ƙananan yara.

People are also reading