Home Back

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Fitar Da Sunayen Wadanda Ake Zargi Da Kashe Sojoji A Delta

leadership.ng 2024/5/9
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Fitar Da Sunayen Wadanda Ake Zargi Da Kashe Sojoji A Delta

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta fitar sunan mutane takwas da ta ke nema ruwa a jallo, wadanda ake zargi da kashe dakarun sojinta 17 a yankin Okuama da ke Jihar Delta.

Daraktan yada labaran rundunar, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana wa manema labarai a safiyar ranar Alhamis.

Ya ce za a yi wa duk wanda ya bayar bayani ko masaniyar inda wadanda ake zargin suke alheri.

Daga cikin wadanda rundunar ta ke nema sun hada da Farfesa Ekpekpo Arthur da Reuben Baru da Akata Malawa David da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe sai kuma wata mata Misis Igoli Ebi.

Janar Buba ya bukaci masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma da ke yankin Neja Delta, su taimaka wa rundunar wajen gano inda wadanda ake zargin suka shiga.

A ranar 14 ga watan Maris ne, wasu matasa suka yi wa wasu dakarun soji da ke aiki a karkashin bataliya ta 181 kawanya, a lokacin da suka je aikin wanzar da zaman lafiya a Okuama, sannan suka yi musu kisan gilla.

A ranar Laraba ne, gawar Sojoji da aka kashe ta isa Abuja, inda aka yi musu jana’iza.

A gefe guda kuma Shugaba Tinubu ya karrama su da babbar lambar yabo ta kasa, tare alkawarin gina wa iyalansu gida a duk inda suke so tare da daukar nauyin karatun ‘ya’yansu har zuwa matakin jami’a.

People are also reading