Home Back

West Ham ta ɗauki ɗan wasan Man Utd Wan-Bissaka kan £15m

bbc.com 2024/10/5
Aaron Wan-Bissaka

Asalin hoton, Getty Images

West Ham United ta ɗauki mai tsaron baya, Aaron Wan-Bissaka daga Manchester United kan £15m.

Tuni ɗan wasan mai shekara 26 ya saka hannu kan ƙwantiragin kaka bakwai da West Ham.

Wan-Bissaka ya koma Manchester United daga Crystal Palace kan £50m a 2019, wanda ya ci ƙwallo biyu a wasa 190 da ya buga wa Red Devils.

Ya zama na takwas da West Ham ta ɗauka kan fara kakar bana da ya haɗa da Jean-Clair Todibo da Crysencio Summerville da Luis Guilherme da Niclas Fullkrug da Wes Foderingham da Max Kilman da kuma Guido Rodriguez.

Ole Gunnar Solskjaer ne ya ɗauki Wan-Bissaka a 2019 lokacin da yake kociyan United, wanda ya ci gaba da taka leda sosai, sai bayan 2021 da Solskjer ya bar ƙungiyar Wan Bissaka ya fara zaman benci.

Ya kasa samun gurbin buga wasannin yadda ya kamata karkashin Erik ten Hag tun daga 2022, koda yake ya yi karawa 64 a kaka biyu karkashin ɗan kasar Netherlands.

United na zawarcin ɗan wasan Bayern Munich, Noussair Mazraoui, amma cinikin ya dogara idan ta sayar da Wan-Bissaka, kenan yanzu za ta yi kokarin kammala sayen ɗan wasan tawagar Morocco.

West Ham za ta fara wasan makon farko a Premier League kakar 2024/25 da Aston Villa ranar 17 ga watan Agusta, yayin da United za ta karɓi bakuncin Fulham ranar 16 ga watan Agusta.

People are also reading