Home Back

Olaf Scholz na Jamus zai gana da shugaban Argentina Milei

dw.com 2024/7/3
Hoto: Abdulhamid Hosbas/AA/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai karbi bakuncin shugaban Argentina Javier Milei a Lahadin nan a birnin Berlin, inda ake sa ran za su tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Ganawar shugabannin biyu masu ra'ayoyi da ke cin karo da juna, za ta mayar da hankali kan batun kasuwanci marar shinge, tsakanin kungiyar tarayyar Turai EU da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Amurka.

Tun da fari dai an tsara yi wa Mr Milei tarba da faretin sojoji tare da taron manema labarai, amma aka soke hakan a cikin kankanin lokaci.

Argentina dai na da dinbin arzikin sinadarin Lithium, wanda Jamus ke matukar bukata domin bunkasa harkokin makamashinta.

People are also reading