Home Back

Hanyoyin Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro a Najeriya – Nuhu Ribadu

premiumtimesng.com 2024/5/17
Hanyoyin Kawo Ƙarshen Matsalar  Tsaro a Najeriya – Nuhu Ribadu

Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa akwai buƙatar yin gagarimin shirin yi wa matsalar tsaro ɗaukar-ɗaki cancak, domin a kawar da matsalar gabaɗaya.

Ribadu ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya ke jawabi a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

A cikin laccar da Ribadu ya bayar, ya yi cikakken bayani dalla-dalla, dangane da tsare-tsaren da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bijiro da su domin daƙile matsalar tsaro.

Ribadu ya bayyana matsalar tsaro a Arewa cewa “murɗaɗɗen al’amari ne wanda ke harɗe da matsalar zamantakewa da matsalar tallalin arziki da kuma matsalar ƙabilannci da batutuwa na addini.

Tinubu Shugaba Ne Mai Gaggauta Ɗaukar Matakan Gaggawa – Nuhu Ribadu:

Nuhu Ribadu, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa irin matakan gaggawa da Shugaba Tinubu ke ɗauka wajen magance matsalolin tsaro su na haifar da ɗa mai ido sosai.

Ribadu ya yi wannan bayani a ranar Alhamis, lokacin da ya ke gabatar da takardar Babban Baƙo mai jawabi a yayin lacca, a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Ya ce, shirin gwamnatin Tinubu na “Fata Nagari Lamiri” (Renewed Hope Agenda), ya samar da cikakken tsare-tsare da matakan daƙile matsalar tsaro.

Maƙalar mai taken: Hanyoyin Shawo Kan Ƙalubalen Matsalolin Tsaro a Arewacin Najeriya”, Ribadu ya bayyana irin ci gaban da aka samu sakamakon gaggauta yin abin da ya dace a duk lokacin da dacewar gaggautawar ce ta dace.

Ya ce ƙalubale ne wanda ya shafi kowa, kuma kowa na ciki, shi ya sa ake haɗa hannu baki ɗaya ake kan samun nasara.

Ya ƙara da cewa yaƙi da matsalolin tsaro abu ne da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da sauran tsare-tsaren magance matsalolin da suka shafi fatara da talauci, rashin aikin yi, kawo ƙarshen ware wasu ba’arin ɓangarorin al’umma ta hanyar jawo su a jika, daƙile yawan tashe-tashen hankulan ƙabilanci ta hanyar ɗarsasa zaman lumana da yalwar arziki a Arewacin Najeriya.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya na sane ya naɗa ‘yan Arewa manyan muƙaman da suka shafi harkokin tsaro, saboda ya shigar da mutanen da ke kusa da inda ake fama da ƙalubalen, domin a samu hanyoyin warware matsalolin sosai da sosai.

“Har yanzu dai da sauran rina a kaba. Ba mu kai ga fita daga waɗannan matsalolin ba tukunna, to amma kuma mun samu gagarumar nasara wajen rage yawan rayukan da ake salwantarwa. Sannan kuma muna ci gaba wajen hana muggan makamai isa hannun mugayen mutane.

“To amma kuma ci gaba da bijiro da hanyoyin amfani da sojoji, siyasa da inganta rayuwar al’umma za su ci gaba da taimakawa a samu nasarar amfani da sojoji.

Da ya ke bayanin rata, tazara da bambancin da ke tsakanin Arewa da Kudu, Ribadu ya kawo shawarar cewa akwai buƙatar a kai ɗauki sosai a wasu ɓangarorin da talauci da rashin aikin yi suka yi kaka-gida.

Ya kuma nuna damuwa dangane da yawaitar safarar muggan makamai a Arewacin Najeriya. Har ya yi nemi a haɗa ƙarfi wajen daƙile wannan mummunar sana’a.

Matsalar Tsaro: Ko Gwamna Lugga Sai Da Ya Sha Fama Da ‘Yan Samame, Cikin 1903 – Nuhu Ribadu:

Da yake ɗauko tarihin rikice-rikicen da ya tirniƙe Arewa, Ribadu ya ce su kan su Turawan mulkin mallaka na Birtaniya ai sun fara tunanin haɗe Arewaci da Kudancin ƙasar nan ce a 1914, saboda buƙatar daƙile ‘yan samame a lokacin masu cin karen su babu babbaka a cikin dazuka.

“Duk da cewa dai batun tattalin arziki ne ke mamaye dalilan haɗe Arewaci da Kudancin ƙasar nan idan ana tattaunawa dalilan haɗe Najeriya, to amma dai daga cikin manyan dalilan akwai dalilan ƙara tsaurara matakan tsaro musamman a yankin Arewa inda Musulmi ke da mafi rinjaye.

“Saboda ko Gwamna Lugga shi kan sa ya sha artabu da ‘yan samame ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba. Sun sha yi masa kwanton-ɓauna shi da tawagar sa. Kuma a lokacin su ne ke tare hanyoyi a cikin dazuka, su na kai samame a cikin ƙauyuka tare da banka wa ƙauyuka wuta, su na kawo gagarimar matsalar tsaro.

“Gwamna Lugga ya sha artabu da ‘yan samame a yankin ƙasar Nupe, Kano da Borgu, har sai da ta kai a dajin Borgu ‘yan samame sun raunata shi. Wannan ya nuna irin yadda aka yi fama da gagarimar matsalar tsaro tun a lokacin.”

Tashin Hankali: Akwai Gogarma-gogarman ‘Yan Bindiga Fiye da 300 a Arewa, Kowane da Sansanin sa – Ribadu:

Ribadu ya bayyana cewa yanzu haka aƙalla akwai sansanin ‘yan bindiga sama da 300 a Arewa, kowane a ƙarƙashin gogarman su. Aƙalla kuma kowane gogarma ɗaya ya na jagorantar gungun mahara matasa 50 abin da ya yi sama, a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.”

Ya ce wannan gagarimar matsala ta ƙara ƙamari ta hanyar safarar muggan makamai a Arewa da ma sauran yankunan Najeriya.

“A baya matsalar mahara ta tsaya ne kawai kan satar shanu. Amma yanzu wasu matsiyatan marasa kishi masu aikata muggan laifuka sun maida lamarin gagarimar hanyar samun maƙudan kuɗaɗe, ta hanyar kai muggan hare-hare da suka haɗa da garkuwa da mutane ana karɓar kuɗaɗen fansa, muggan hare-haren ƙona gidaje da dukiyoyin jama’a da sauran su.

“Wannan ya kawo mummunar tawayar tattalin arziki, wanda ya faru a daidai lokacin da gwamnati ta kauda kai daga dalilan da ke sa mahara ƙara ƙarfi ta hanyar mallakar muggan makamai.”

Matsalar Tsaro A Arewa: Sai An San Mafarin Ciwo Ake Gane Maganin Sa – Ribadu:

Ribadu ya ce magance matsalar ‘yan bindiga a Arewa na buƙatar ba amfani da jami’an tsaro kaɗai ba, tilas sai an fahimci tushe da asalin rikicin,” cewar Ribadu.

Matsalar Tsaro A Arewa: Wasu Daga Cikin Tushen Matsalolin – Ribadu:

Ribadu ya ce kaɗan daga cikin manyan tushe da musabbabin matsalar tsaro a Arewa sun haɗa da: rikice-rikicen gonaki, sauyin rayuwar al’ummar karkara, canjin yanayi, cusa tsautsauran ra’ayi da mummunar aƙida, ƙarancin jami’an tsaro, samun damar mallakar makamai a sauƙaƙe, cin hanci da rashawa, rashin adalci da kuma fantsamar ɗimbin jama’a daga ƙasashe masu maƙwautaka da Najeriya, wanda hakan ke samar da damar karakainar mahara da ‘yan bindiga.

Nasabar Matsalar Tsaro Da Rashin Ƙarfin Tattalin Arziki A Arewa – Nuhu Ribadu:

Haka kuma Ribadu ya nuna matuƙar damuwa, ganin cewa matsalar tsaro a Arewa ta na da nasaba ta kurkusa da rashin ƙarfin tattalin arzikin yankin da kuma yadda ake fama da yawan magidantan da ba su da ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar kan su ko ta iyalin su (HDI).

Ya ce wannan matsala ta yi tasiri sosai wajen haifar da matsalolin rashin ilmi, kiwon lafiya da kuma damammakin bunƙasa tattalin arziki ga ɗaiɗaikun mutane ko al’umma bakiɗaya.

Matsalar Tsaro A Arewa: Hanyoyin Da Za A Taru A ‘Kashe Mahaukacin Kare’ – Nuhu Ribadu

Ribadu ya ce akwai matuƙar buƙatar yi wa wannan babbar matsala taron-dangi, ta hanyar haɗin ƙarfi da sojoji, tsarin siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, tare kuma da haɗin kai da ƙasashen tsallake da yin amfani da al’umma mazauna karkara.”

Ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu ke fuskantar matsalar hanyoyin daƙile matsalar tsaro, ta hanyar bijiro da tsare-tsare a ƙarƙashin Shirin Fata Nagari Lamiri, abin da ya ƙunshi, ” inganta ƙarfin jami’an tsaro, bijiro da tsarin kula da sa-ido a cikin al’umma ta hanyar amfani da mutanen cikin yankuna, inganta hanyoyin ƙarfafa rayuwa, tattaunawa tsakanin al’umma yankuna domin ƙarfafa sasanci a tsakanin masu husuma da sauran su.”

People are also reading