Home Back

Likita ya kirkiro wata hanyar warkar da radadin ciwon kafa da masu fama da cutar sikila ke fama da shi na dindindin

premiumtimesng.com 2024/5/20
Likita ya kirkiro wata hanyar warkar da radadin ciwon kafa da masu fama da cutar sikila ke fama da shi na dindindin

Wani kwararre likitan fida dake aiki da asibitin Hafar Al-batin dake kasar Saudiya Ayodele Ogunkeyede ya bayyana cewa ya gano maganin warka da ciwon kafa da masu fama da cutar sikila ke yawan fama da shi (Leg ulcers).

Ogunkeyede ya ce hanyar da ake bi kuwa shine nada kafar maralafiya da wani bandeji na musamman sannan a rika yi masa/mata tausa domin jinin da ya daskare ya ki wucewa yana zagaya wa da kyau.

Ya ce yin haka hanya ce zai taimaka wajen inganta zagayen jini a duka sassan jikin maralafiya.

Likitan ya ce wannan hanya ce da ya gano na warkar da ciwon kafa a cikin watanni uku zuwa shida da masu fama da cutar kan yi shekaru suna jinya.

Ya ce tun a shekarar 2015 ne ya fara gano wannan hanya na warkar da ciwon amma kuma saboda tsadar wannan bandeji ya sa samun maganin ke wahala ballantana har a yi mafani da shi.

” Amma zuwa yanzu bandejin ya yi saukin da za a iya siya a yi amfani wa maralafiya. Kuma cikin dan kankanin lokaci kafa zai mike ba za a sake samun wannan matsala ba.

Ogunkeyede ya ce zuwa yanzu jami’an asibiti sun fara samun horo kan yadda za su rika amfani da wannan bandeji.

People are also reading