Home Back

Akintoye da Igboho sun aika wa Tinubu wasiƙar buƙatar ficewar Yarabawa daga Najeriya

premiumtimesng.com 2024/5/15
Ba mu son ganin ko Bafulatani ɗaya tal a yankin Yarabawa daga ranar litinin – Sunday Igboho

Ƙungiyar Neman Ƙasar Yarabawa Zalla, ƙarƙashin jagorancin Banji Akintoye, tare da gogarman korar Fulani daga yankin Yarabawa, Sunday Igboho, sun aika wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu buɗaɗɗiyar wasiƙar sanar da shi buƙatar ƙabilar Yarabawa, wadda ta ƙunshi neman ficewa daga Jamhuriyar Najeriya salum-alum a cikin ruwan sanyi.

A cikin wasiƙar wadda Akintoye da Ibgboho suka sa wa hannu kuma suka watsa a ranar Lahadi, sun yi kira ga Shugaban Ƙasa ya kafa kwamitin tattauna ficewar Yarabawa daga Najeriya, wanda zai tattauna da su, a cikin watanni biyu masu zuwa.

Wannan kiraye-kirayen na su ya zo ne makonni biyu bayan wasu Yarabawa ‘yan ta-kife masu ƙumajin neman kafa ƙasar Yarabawa zalla, sun mamaye Sakateriyar Gwamnatin Jihar Oyo.

Idan masu karatu ba su manta ba, Akintoye da Igboho sun nesanta kawunan su da abin da ya faru a Badun.

‘Mun Gaji Da Zama Ƙasa Ɗaya Da Fulani’ – Masu Rajin Kafa Ƙasar Yarabawa:

CIkin wasiƙar da Akintoye da Igboho suka aika wa Tinubu, sun ci gaba da cewa sun gaji da zama ƙasa ɗaya da Fulani masu kashe Yarabawa ba ji ba gani.

Sun ce daga 2015 zuwa yau Fulani sun Yarabawa 29,000, kuma babu ranar dainawa.

Wasiƙar ta ƙara da cewa Yarabawa ba su yi amanna da duk wani sabon tsarin da za a bijiro da shi domin Sake Fasalin Najeriya ba, saboda a cewar su, tsarin ba zai iya hana Fulani ci gaba da kashe Yarabawa ba.

Dangane da haka ne su ke kira a zauna zaman tattaunawa ficewar yankin Yarabawa daga Najeriya, a cikin ruwan sanyi, tare da tsoma ƙungiyoyin duniya a matsayin masu sa-ido, wato irin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Ƙungiyar Ƙasashen Afrika (AU) da kuma ECOWAS.

“Mun aiko wa Shugaban Ƙasa wannan wasiƙa a madadin miliyoyin ‘yan ƙabilar Yarabawa zalla a nan cikin Najeriya da kuma ɗimbin su da ke zaune ƙasashen waje.

“Mun aiko da wannan wasiƙa a matsayin tunatarwa kan wasiƙar da muka fara aikawa a ranar 6 ga Agusta, 2022, wadda muka aika wa Shugaban Ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari, a lokacin shi ke kan mulki.”

People are also reading