Tsohon Sanata Ya Fadi Kuskuren Buhari da Ya Kamata Tinubu Ya Kiyaye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba da fifiko wajen duba cancanta yayin naɗa muƙamai.
Shehu Sani ya gargadi shugaban ƙasan da kada ya yi irin kuskuren magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya ce a lokacin gwamnatin Buhari na shekara takwas tsakanin 2015 zuwa 2023, an nuna son zuciya wajen naɗa muƙamai amma duk da haka ba a samar da sakamako mai kyau ba.
"Zan shawarci shugaban ƙasa Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan kada ya tafka kura-kurai na shugaba Buhari, kuma na yi imanin cewa yana da ƙwarewar da zai fahimci hakan."
"A ƙarƙashin Shugaba Buhari, akwai ministoci da aka naɗa a kan muƙamansu tsawon shekaru takwas, sun kasance tare da shi a zangon farko da na biyu, kuma babu wani garambawul na majalisar ministoci."
"Ko da an cire wani, sai an ɗauki watanni uku zuwa huɗu kafin a maye gurbin minista. Haka aka gudanar da mulkin ƙasar."
"A ƙarƙashin Buhari mun ga ƙololuwar son zuciya inda aka naɗa mutane muƙamai kuma aka barsu ko da ba su yi komai ba."
- Sanata Shehu Sani
Ya bayyana cewa idan Tinubu yana son samun sakamako mai kyau, cancanta ya kamata ta zama abin da zai fi bayar da muhimmanci a kai.
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga shugabannin Arewa da su ba ilmi muhimmancin gaske.
Sanata Shehu Sani ya buƙace su da su ɗauki ilimi da gaske domin kaucewa rugujewar makarantun gwamnati.
Asali: Legit.ng