Home Back

Masu kwaɗayin kujerar shugabancin Najeriya su ɗau kaddara, kujera dai ta Tinubu ce har bayan 2027 – Ganduje

premiumtimesng.com 2024/5/18
Masu kwaɗayin kujerar shugabancin Najeriya su ɗau kaddara, kujera dai ta Tinubu ce har bayan 2027 – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shugaban Kasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban Najeriya har bayan 2027.

Ganduje ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC a sakatariyar Jam’iyyar da ke Abuja.

Ganduje ya ƙara da cewa tun ba a kai ko ina ba jam’iyyun adawa sun fara kerma tsoron yin gaba da gaba da APC a zabuka masu zuwa bayan ɗan karan kayin da suka sha a zaɓen 2923.

” Jam’iyyar NNPP sun fi duk jam’iyyun Kiɗimewa. Sai tsalle-tsalle suke yi ba su nan ba su can. Kuma wai fa duk shirin 2027 su ke yi.

” Abinda zan faɗi musu kuwa shine kujerar shugaban kasa ta Tinubu, ba a buƙatar canja ta. Saboda tun yanzu sun sha kasa. Kuma ku sani cewa muna sane da waɗanda ke kokarin kawo ruɗani a jam’iyyar mu, kawai don a rika cewa an samu ɓaraka.

” Su sani muna nan tmɗaure tamau kamar yadda aka san mu, ba bu abinda ya girgiza ko yake bamu tsoro. Su je can su cigaba da kulla makircin su mu kuma nuna nan muna kara shiri.

” Idan da za ku yi nazarin yadda abubuwa ke faruwa a jihar Kano za ku ga cewa ko su kansu jam’iyyar Adawa a rabe suke.

People are also reading