Home Back

Hotunan yadda aka gudanar da bikin babbar Sallah a sassan duniya

rfi.fr 2024/7/5

A jiya Lahadi ne aka gudanar da bikin babbar Sallah a sassan duniya, wanda aka saba gudanar da shi a duk ranar 10 ga watan Musuluci na Zhul-hajj, wato kwana guda da hawan Alhazai Arafa a birnin Makka da ke Saudiyya. Wannan shafin na ɗauke da wasu kayatattun hotuna kan yadda aka gudanar da bikin a sassan duniya.

Wallafawa ranar: 17/06/2024 - 16:39

Minti 3

Wasu ƴan matan Kenya kenan ke addu'a bayan kammala Sallar Idi a birnin Nairobi
Wasu ƴan matan Kenya kenan ke addu'a bayan kammala Sallar Idi a birnin Nairobi REUTERS - Monicah Mwangi
Masu aikin fiɗan nama a birnin Mogadishu na Somalia
Masu aikin fiɗan nama a birnin Mogadishu na Somalia REUTERS - Feisal Omar
Yadda ake rarraba naman layya ga maɓukata a Indonesia.
Yadda ake rarraba naman layya ga maɓukata a Indonesia. REUTERS - Riska Munawarah
Matan Indonesia kenan ke Sallar Idi a Meulaboh.
Matan Indonesia kenan ke Sallar Idi a Meulaboh. via REUTERS - ANTARA FOTO
Musulmai na shiga Masallacin Bhaitul Mukarram a Bangladesh don Sallar Idi
Musulmai na shiga Masallacin Bhaitul Mukarram a Bangladesh don Sallar Idi REUTERS - Mohammad Ponir Hossain
Musulmai sun yi sujjada a yayin Sallar Idi a birnin Abidjan na Ivory Coast.
Musulmai sun yi sujjada a yayin Sallar Idi a birnin Abidjan na Ivory Coast. REUTERS - Luc Gnago
Musulmai na sauraren huɗuba a birnin Nairobi bayan kammala Salla.
Musulmai na sauraren huɗuba a birnin Nairobi bayan kammala Salla. REUTERS - Thomas Mukoya
Wasu ƴan mata na hawa lilo don murnar babbar Sallah a Nairobi
Wasu ƴan mata na hawa lilo don murnar babbar Sallah a Nairobi REUTERS - Monicah Mwangi
Musulman birnin Moscow na jiran isowar liman domin Sallar Idi
Musulman birnin Moscow na jiran isowar liman domin Sallar Idi REUTERS - Yulia Morozova
Masu Sallar idi a birnin Mosul na Iraqi.
Masu Sallar idi a birnin Mosul na Iraqi. REUTERS - Khalid Al-Mousily
Falasɗinawa sun yi Sallar Idi a cikin ɓuraguzai a Masallacin Rahma da hare-haren Isra'ila suka lalata.
Falasɗinawa sun yi Sallar Idi a cikin ɓuraguzai a Masallacin Rahma da hare-haren Isra'ila suka lalata. REUTERS - Mohammed Salem
Falaɗinawa na Sallar Idi a Khan Younis na Zirin Gaza.
Falaɗinawa na Sallar Idi a Khan Younis na Zirin Gaza. REUTERS - Mohammed Salem
Wani ɓangare na Falasɗinawa da ke Sallar idi cikin ɓuraguzai.
Wani ɓangare na Falasɗinawa da ke Sallar idi cikin ɓuraguzai. REUTERS - Mohammed Salem
People are also reading