Home Back

‘Matsayar Mu Kan Rahoton Yarjejeniyar Samoa’ – Daily Trust

premiumtimesng.com 2024/8/23
‘Matsayar Mu Kan Rahoton Yarjejeniyar Samoa’ – Daily Trust

Jaridar Daily Trust ta bayyana matsayin ta dangane da rahoton da ta buga kan Yarjejeniyar Samoa, wanda bai yi wa Gwamnatin Tarayya daɗi ba, har gwamnatin ta yi barazanar maka jaridar kotu.

Jaridar ta fitar da sanarwar mai ƙunshe da cewa: “Ministoci biyu da wasu masu sharhi sun ragargaji jaridar mu, dangane da labarin da muka buga kan Yarjejeniyar Samoa, har ma dangane da wasu rahotannin da muka taɓa bugawa a baya.

“To mun bi waɗannan jami’an gwamnati a tsanake ta hanyar nazarin abin da suka faɗa, har ma abin da ba su faɗa ɗin ba. Amma dai za mu buga komai baki ɗaya, domin taskace bayanan, ko don gaba.

“To kuma mun amince da inda aka samu tasgaro a ɓangaren rahoton da muka buga, musamman kan yarjejeniyar, saboda wasu ƙwararru sun nusasshe mu, kuma za mu sake nazarin abin da muka buga, tare da ɗaukar matakan da suka dace.

“To kamar yadda editocin mu suka fahimci lamarin, ita dai Yarjejeniyar Samoa wadda Najeriya ta sa wa hannu, ta faɗaɗa ma’anar ‘yancin kowane jinsi daga ɗabi’ar mu’amala ta namiji da mace, zuwa sabuwar ma’anar da aka cusa LGBTQ a ciki (Maɗigo, Mata-maza, ‘Yan Luwaɗi da Masu Canja Jinsin Halittar su). Kuma daga nan ne ce-ce-ku-cen ya taso.

“Idan har wannan yarjejeniyar babu yaɗa wannan ‘yanci, wanda ƙasashen Turai na Yamma sun daɗe da karɓar sa hannu bibbiyu, to mun yi wa ma’anar mummunar fassara, kuma a shirye muke da mu nemi afuwa ga gwamnati da kuma jama’a baki ɗaya.

Mu na buƙatar ƙwararrun da suka samu cikakken horo da gogewa su fito su yi hukunci, mu kuma sai mu ɗora a kan sikeli, sannan mu buga dukkan hukuncin da ɓangarori suka yanke a tattauna batun, har ma da na ita kan ta gwamnatin.

Mu na so mu ƙara da cewa a wannan labari na Yarjejeniyar Samoa da muka buga, kamar a sauran labarai a tsawon shekaru 26, Daily Trust ta riƙa yin matuƙar taka-tsantsan.

“Kuma ya na da kyau mu warware wata mummunar fahimta da Ministan Yaɗa Labarai ya yi kan wasu labarai da Daily Trust ta buga can baya.”

Cikin sanarwar da Sakatariyar Kamfani kuma Mai Bada Shawara a Fannin Shari’a ta Daily Trust, Maryan Aminu-Bello ta sa wa hannu, ta yi magana kan wasu labaran da ministan ya yi ƙorafi a kan su. Kuma ta kare kamfanin kan cewa babu ƙage ko ɓatanci a cikin labaran.

A ƙarshe ta ce tun cikin 1998 aka kafa Daily Trust, jaridar ta yi zamani da shugabannin Najeriya daban-daban har shida, yanzu Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne na bakwai.

Ta ce jaridar na nan a kan gaskiya ba tare da nuna son rai wajen isar da saƙonnin ta ba.

People are also reading