Home Back

Rundunar Sojoji Ta Sha Alwashi Kan Kisan da Aka Yiwa Sojoji a Abia, Ta Fadi Masu Hannu a Harin

legit.ng 2024/7/3
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan kisan da aka yiwa sojoji biyar a jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Kudu
  • A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na DHQ ya fitar, ya ce rundunar sojojin za ta mayar da martani mai zafi kan kisan jami'an tsaron
  • DHQ ta ɗora alhakin kisan jami'an tsaro a kan ƙungiyar da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), zargin da ƙungiyar ta fito ta musanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta lashi takobin mayar da martani mai zafi kan kisan da aka yi wa sojoji biyar a jihar Abia.

An dai hallaka sojojin ne a lokacin ranar tunawa da ƙasar Biafra wacce ƙungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta ɗauki nauyi a ranar Alhamis.

Rundunar sojoji ta yi magana kan kisan sojoji a Abia
Rundunar sojoji ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan kisan sojoji a Abia Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Twitter

Su wa ke da hannu a kisan sojojin?

Rundunar sojojin ta zargi ƙungiyar IPOB da ƙungiyar ESN da laifi a harin da aka kai a mahaɗar Obikabia dake ƙaramar hukumar Obingwa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaron, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a jiya Juma'a, ƙungiyar ta fito ta ce ba ta da hannu a kashe-kashen da aka yi na sojojin.

Daraktan yada labarai DHQ, Manjo Janar Edward Buba, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ƴan ta'addan sun zo cikin wasu motoci uku sannan suka hallaka sojojin waɗanda ke baki aiki a wajen shingen binciken.

Ya ce, an tura sojojin ne domin su tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma kare mutane, sai kawai ƴan ta’addan suka far musu tare da kashe su, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Wane mataki sojoji za su ɗauka?

"Rundunar sojoji ta yi alhinin mutuwar waɗannan sojoji domin kowane soja da aka rasa a fagen daga babban rashi ne."
"A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da bincike dangane da harin."
"Don haka, ya zama wajibi sojoji su mayar da martani kan wannan mummunan ɗanyen aiki da aka yi wa jami'an tsaron"
"Sojoji za su yi kakkausan martani kan kisan da aka yi. Za mu yiwa ƙungiyar matsin lamba domin tabbatar da cewa an kawo ƙarshenta."

- Manjo Janar Edward Buba

Gwamna ya sa tukwici kan kisan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya sanya tukuicin Naira miliyan 25 kan wadanda suka kashe sojojin Najeriya biyar a mahadar Obikabia, tsaunin Ogbor a Aba.

Gwamnan ya yi alƙawrin cewa duk wanda ya taimaka da sahihan bayanai har aka cafke makasan za a ba shi waɗannan kuɗaɗe N25m a matsayin lada.

Asali: Legit.ng

People are also reading