Home Back

SHEKARAR FARKON MULKIN TINUBU: An kashe ‘yan Najeriya 4,500, an yi garkuwa da mutum 7000

premiumtimesng.com 2024/9/27
ZAMAN DARDAR: Yan Bindiga sun sace babbar ‘yan kasuwa a Tegina, sun yi barazanar dawuwa su sace sauran attajiran garin

Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin daƙile matsalar tsaro, a lokacin da yake jawabin karɓar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ba wannan ne karo ɗaya tilo da Tinubu ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro ba. Ya sha faɗa kafin zaɓe da kuma bayan kammala zaɓe, sau da dama.

Sai dai kuma ga shi Shugaba Tinubu ya cika shekara ɗaya kan mulki, amma har yanzu matsalar tsaro sai ƙara balbala take yi, kamar wutar daji.

Duk da dai shekara ɗaya ta yi kaɗan a auna nasarar wannan gwamnatin a fannin tsaro, amma dai babu wani ci gaba da aka samu a fannin tsaro, daga inda mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya bar matsalar.

Tsakanin 29 ga Mayu 2023 zuwa 11 ga Mayu 2024, ƙididdigar alƙaluman adadin mutanen da aka kashe sun kai 4,556, sannan kuma an yi garkuwa da mutum 7,086. Wata Cibiyar Ƙididdigar Alƙaluman Rikice-rikice mai suna ‘Armed & Event Data Project (ACLED) ta fito da wannan ƙididdiga.

Shekarar Farko Ta Mulkin Tinubu: Jadawalin Rasa Rayuka Da Garkuwa Da ‘Yan Najeriya:

Kisan Mutum 1,475, Garkuwa Da Mutum 4,343 A Arewa Maso Yamma:

Jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara ne zafafan jihohin da tashe-tashen hankula suka fi rincaɓewa, inda aka samu rahotannin hare-hare 551 daga cikin 718 daga aka kai yankin baki ɗaya, cikin farkon shekara ɗaya ta mulkin Tinubu.

Arewa Ta Tsakiya:

A hare-haren da rigingimun manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya guda 552 cikin shekarar farko an yi rashin mutum aƙalla 1,444, cikin su kuwa har da sojoji da ‘yan sa-kai.

Sannan kuma an yi garkuwa da mutum 1,321a yankin na Arewa ta Tsakiya.

Arewa Maso Gabas: Kisan Mutum 816, Garkuwa Da Mutum 668 A Shekarar Farkon Mulkin Tinubu:

A Barno, Yobe da Adamawa an kashe mutum 816, aka yi garkuwa da mutum 688 a hare-hare 408.

Kashe-kashen ‘Yan Aware Da ‘Yan Ƙungiyar Asiri A Kudu:

An samu rahotannin munanan tashe-tashen hankula har sau 231 cikin shekarar farkon mulkin Tinubu. A Kudu maso Kudu an kashe mutum 336, an yi garkuwa da mutum 295.

Akwai tashe-tashen hankula na ‘yan aware da kisa ba bisa haƙƙin shari’a ba na mutum 310 a Kudu maso Gabas, inda kuma aka yi garkuwa da mutum 214.

Kashe-kashe A Kudu Maso Yamma:

Akwai rigingimun ‘yan ƙungiyar asiri, ‘yan bindiga da sauran manyan laifuka daban daban. An kashe farar hula 172, aka yi garkuwa da 225.

Manyan Munanan Hare-haren Ta’addanci A Shekara Ɗaya Na Mulkin Tinubu:

Ko watanni uku dindi Tinubu bai cika kan mulki ba, Boko Haram suka kashe Sojojin Najeriya 36 a Jihar Neja, a ranar 14 ga Agusta, 2023.

A wannan ranar ce dai gogarman ta’addanci Dogo Giɗe ya kakkaɓo jirgin sojojin Najeriya, wanda ya ɗauko sojojin da aka ji wa ciwo da gawarwakin waɗanda suka rasa rayukan su a kwanton-ɓaunar da maharan suka yi masu.

Duk da Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta ce hatsari ne jirgin ya yi ba kakkaɓo shi aka yi ba, an nuno su Dogo Giɗe a wurin jirgin su na ɗaukar hotuna da bidiyo, wanda suka watsa cewa su ne suka kakkaɓo jirgin.

Watanni uku bayan nan kuma sai mummunan kashe-kashe ya ɓarke a Bakkos da Mangu cikin Jihar Filato, inda aka kashe sama da mutum 100 a jajibirin Kirsimeti.

Cikin watan Maris, 2024, ‘yan ta’adda sun sace ɗalibai 137 daga firamare da sakandare ta Kuriga, a Ƙaramar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna. An saki ɗaliban makonni biyu bayan an biya maƙudan kuɗaɗen fansa.

A cikin watan ne kuma aka kashe Sojojin Najeriya 15, garin Okuama, cikin Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu, a Jihar Delta.

Ko Ana Samun Nasarar Yaƙi Da Ta’addanci Kuwa?:

A makon jiya ne Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya bayyana cewa, “Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe Boko Haram da ‘yan bindiga har 9,300 a cikin shekara ɗaya. An kama kimanin 7,000, sannan kuma an damƙe 4,641, duk a cikin shekara ɗaya.”

Sai dai kuma wani masanin dabarun tsaro mai suna Kabiru Adamu, ya ce har yanzu Shugaba Tinubu bai magance musabbabin matsalolin da ke haddasa matsalar tsaro ba.

People are also reading