Home Back

Atiku da Ribadu duk sun ci albarkacin Tinubu, a lokutan da aka riƙa yi masu bi-ta-ƙulli – Kashim Shettima

premiumtimesng.com 2024/6/29
Atiku da Ribadu duk sun ci albarkacin Tinubu, a lokutan da aka riƙa yi masu bi-ta-ƙulli – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu duk sun ci albarkaci da moriyar Shugaba Bola Tinubu, a can lokutan baya, sa’adda gwamnatin baya ta riƙa yi masu bi-ta-ƙullin siyasa.

Shettima ya ce akwai lokacin Atiku ya riƙa karakaina a gidan Tinubu da ke kan Titin Bourdillion a Legas, lokacin da aka takura masa, aka tsangwame shi har ya fice daga PDP.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya furta hakan Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Alhamis.

Ya tuna cewa lokutan da mutanen Tinubu ɗin ke ta gugumarar samun mulki a Abuja, Asiwaju ya riƙa amfani da kuɗin sa, kayan sa da alfarmar sa da lokacin sa domin tabbatar da nasarar dimokraɗiyya a Najeriya.

“Shugaba Tinubu ya zama uwa abin share hawayen manyan ‘yan siyasar da aka riƙa yi wa bi-ta-ƙulli ana hantarar su, ana hana su shan inuwar siyasa. Lokacin da aka riƙa hantarar Atiku Abubakar a PDP, sai ya koma ya na karakaina a gidan Tinubu, inda aka ba shi cikakken goyon bayan da ya fito takarar shugabancin ƙasa.

“Bayan shekara huɗu kuma Asiwaju ya sake tattago wani ɗan Najeriya, ya goya masa baya domin ya yi takarar shugabancin ƙasa, wato Nuhu Ribadu, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa a yanzu.

“Don haka ba wai haka kawai tashi Asiwaju Bola Tinubu ya yi ta rana tsaka ya kama hanyar shiga Fadar Aso Rock ba. Ya shafe shekaru ya na jihadin nuna kishin kafa nagartacciyar gwamnati a ƙasar nan,” inji Shettima.

Shettima ya nuna farin cikin cewa duk wani ƙusa a siyasar Jihar Ekiti, ya na tare da Gwamna Biodun Oyebanji, domin ƙoƙarin bunƙasa jihar.

Da yake magana kan Cibiyar Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (MSMEs) ya ce wurin ya samar da masu hada-hadar kasuwanci da masu zuba jari daga fannoni daban-daban a faɗin ƙasar nan.

“Mun yi farin cikin samun haɗin kai daga SMEDAN, NEXIM, ITF, NAFDAC da sauran su. Sun zo domin su bayar da shawarwari da kuma gudanar da yadda ayyuka za su riƙa tafiya.”

People are also reading