Home Back

Wuce Gona da Irin Isra’ila: Isra’ila Ta Farmaki Makarantar Majalisar Dinkin Duniya a Gaza

legit.ng 2024/10/5
  • Sojojin Isra’ila sun sake kai mummunan hari a wani yankin Gaza, inda suka hallaka fararen hula da basu ji ba basu gani ba
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kashe mata da yara da masu jinya a cikin wata makaranta
  • Tun watan Oktoban bara ake ci gaba da samun hargitsi a yankin na Gaza bayan sake barkewar yaki tsakanin Hamas da Isra'ila

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Zirin Gaza - Gwamnatin Hamas a Gaza ta ce wani hari da Isra’ila ta kai ranar Asabar kan wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa inda dubban ‘yan gudun hijira suke boye ya kashe mutane 16.

Rundunar sojan Isra’ila ta ce jiragen samanta sun kai harin ne kan “'yan ta’adda” da ke aiki a kusa da makarantar Al-Jawni a Nuseirat, tsakiyar Gaza.

Isra'ila ta saki bama-bamai kan makarantar UN
Isra'ila ta kai hari kan makarantar majalisar dinkin duniya | Hoto: Anadolu Asali: Getty Images

Ma’aikatar lafiya ta yankin da Hamas ke jagoranta, wadda ta yi Allah-wadai da harin da ta kira “mummunan kisan kiyashi,” ta ce an kai mutum 50 asibiti daga makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin mutanen da aka jefa a hadari

Kimanin mutane 7,000 ne suke boye a makarantar a lokacin harin, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin Hamas ya bayyana. Mutane da dama sun kutsa cikin baraguzan gine-ginen don neman wadanda suka tsira bayan harin.

Ofishin yada labaran ya ce makarantar tana karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), kuma mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu “yara, mata, da tsofaffi” ne.

Martanin Isra’ila kan harin da ta kai kan farar hula

Rundunar sojan Isra’ila ta ce:

“Mun kai hari kan wasu ‘yan ta’adda ne da ke boye a cikin gine-ginen da ke yankin makarantar UNRWA Al-Jawni.”
“Wannan wuri ya kasance maboya kuma cibiyar gudanarwa da shirya hare-hare kan sojojin IDF da ke aiki a cikin Gaza.”

Hakazalikam Isra’ila tana mai jaddada cewa ta “dauki matakai don rage tasirin jikkatar fararen hula” a yayin harin, inji rahoton Reuters.

Hare-haren Isra’ila na kashe fararen hula

A baya, UNRWA ta ce biyu daga cikin ma’aikatanta sun mutu a wani hari a Al-Bureij, wanda shima yake a tsakiyar zirin Gaza, rahoton Al-Jazeera.

Masu aikin agaji sun ce mutane 10, ciki har da ‘yan jarida uku, sun mutu a wani hari da aka kai kan wani gida a Nuseirat.

Mai magana da yawun hukumar farar hula Mahmdu Bassal ya bayyana cewa:

“Babu wani wuri mai aminci a Gaza.”

Tun bayan rikicin da ya barke tsakanin sojojin Hamas da Isra’ila zirin gaza ke cikin tashin hankali, inda aka kashe daruruwan fararen hula Falasdinawa.

Bayanai kan kitimurmurar Isra'ila da Hamas

Idan muka waiwaya baya, yakin Isra’ila da Hamas ya samo asali ne shekaru da dama, amma a ‘yan watannin baya abubuwa suka kara rikicewa.

A watan Oktoban bara, an samu aukuwar harin da ya tunzura Isra’ila har ta kai ga suka kara kaimi wajen yiwa Falasdinawa kisan kare dangi, kamar yadda masu sharhi ke fadi.

A rahotonmu na baya, mun tattaro maku muhimman lokuta da ya kamata ku kiyaye game da yakin Hamas da Isra’ila.

Asali: Legit.ng

People are also reading