Home Back

Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahoton faɗuwar jirginta

legit.ng 3 days ago
  • Rundunar sojin saman Najeriya tace babu jirginta mai saukar ungulu da yayi haɗari a safiyar Litinin
  • Kakakin NAF ya tabbatar da cewa jirgi mara matuƙi ne yayi hadari a kauyen Rumji, inda babu nisa da sansaninta
  • Gabkwet yace wannan ƙaramin koma-bayan ba zai tsayar da ayyukan da hukumar ke yi bana tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Hukumar rundunar sojin saman Najeriya ta ce wani daga cikin jiragenta na sama mara matuƙi ne yayi haɗari a Kaduna, ba jirgin samanta mai saukar ungulu ba.

Ta kuma ƙara da cewa, ta fara bincike don tabbatar da abinda ka iya kawo haɗarin, inda ta ƙara da cewa babu ko mutum ɗaya da ya samu rauni tun bayan rikitowar jirgin.

NAF ta musanta yin hadarin jirginta mai saukar ungulu a Kaduna. Hoto: Nigerian Air Force
Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahoton faɗuwar jirginta Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgi mai saukar ungulu mallakin NAF an sanar da faɗuwarsa a sa'o'in farko na ranar Litinin a ƙauyen Tami dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Ganau ba jiyau ba wanda ya buƙaci a boye sunansa ya sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru wurin ƙarfe 5 na subahi, lamarin da ya tashi hankalin mazauna yankin.

Rahoton PM News ya bayyana cewa, amma yayin martani ga lamarin, kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, a wata takarda da ya fitar, ya tabbatarwa da 'yan Najeriya "ƙaramin koma-baya" ba zai hana cigaban aikin da ake yi ba

Wani sashi na takardar yace:

"Akasin rahotannin da ke shafukan sada zumunta tare da wasu kafofin yaɗa labarai, cewa jirgin NAF mai saukar ungulu yayi haɗari a Kaduna a safiyar yau, 1 ga Yulin 2024, ina sanar da ku cewa babu haɗarin da ya faru.
"A maimakon hakan, wani jirgin NAF ne mara matuƙi ya fuskanci matsala bayan ya tashi domin fara aiki a wani wuri kusa da ƙauyen Rumji kuma mai nisan kilomita 15 daga sansaninmu."

Ya cigaba da cewa:

"Tun jirgi ne mara matuƙi, babu wanda ya samu rauni a sama ko a ƙasa. An fara bincike tun bayan faruwar lamarin don tabbatar da abinda ya kawo haɗarin.
"'Yan Najeriya su tabbatar da cewa, ƙaramin koma-baya ba zai hana ayyukan da ake yi ci gaba ba ta kowacce hanya."

An yi artabu tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a Abuja

A wani rahoto na daban, an yi ruwan alburusai tsakanin jami'an tsaro da miyagun 'yan bindiga a babban birnin tarayyar Najeriya ta Abuja.

Lamarin mara daɗi ya faru ne a yankin Bwari dake babban birnin tarayyar inda 'yan bindigan suka yi yunƙurin garkuwa da wasu yara.

Asali: Legit.ng

Autres articles lus