Tinubu Zai Dauki Mataki Kan Jami'an Hukumomi da Ke Bincike a Filayen Jiragen Sama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya za ta rage yawan jami'an tsaro da ke binciken kayayyaki a filayen jiragen sama.
Hukumar kula da jiragen sama ta FAAN da ofishin mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro domin tabbatar da haka.
Hukumar ta ce za ta rage yawan jami'an ne daga hukumomi daban-daban a filayen jiragen saman, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FAAN ta ce ta dauki matakin ne domin saukaka tafiye-tafiye yayin da fasinjoji ke kokawa kan yawan binciken a filayen jiragen saman Najeriya.
Babbar manajan hukumar, Olubunmi Kuku ita ta bayyana haka a jiya Asabar 4 ga watan Mayu a Legas.
Kuku ta ce sun yi haɗaka da ofishin NSA domin rage yawan binciken da ake yi a filayen jiragen sama, cewar BusinessDay.
Babbar manajan ta ce za su yi haɗaka wurin amfani da na'urar CCTV a ofis domin tabbatar da ingancin aikinsu.
Har ila yau, Kuku ta ce sun yi magana da Nuhu Ribadu domin ganin an dakile matsalar da ta addabi matafiya.
"Abin ya wuce batun FAAN, akwai hukumomi da dama a filayen jiragen sama da suke yin bincike kan matafiya wanda ya yi yawa."
"Akwai hukumomi kamar NDLEA da Kwastam da kuma EFCC da sauransu da ke cike a filayen jiragen sama domin bincike daban-daban."
- Olubunmi Kuku
Kuku ta ce suna kokarin rage yawan jami'an hukumomi da ke bincike domin inganta yadda za a ci gaba da duba fasinjoji da kayayyakinsu.
Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana tsare-tsaren da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.
Shettima ya ce yanzu ba lokacin zargin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ne illa hanyar neman mafita ga matsalolin ƙasar.
Asali: Legit.ng