Home Back

Gwamnati ta hana ‘yan sanda yin kutse cikin wayoyin mutane lokacin sintiri

premiumtimesng.com 2024/5/3
Masu bata lokaci a soshiyal midiya sun zo duniya a banza, za su tafi a wofi – Oyedepo

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo Funsho Adehboye ya hana ‘yan sanda kwacewa da duba woyoyin hannu na mutane yayin da suke sintiri a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya sanar da haka a shafin sada zumunta na rundunar dake yanar gizo a makon jiya.

“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo ya gargadi jami’an rundunar da su daina wannan aika-aika, domin babban sufeton ‘yan sandan ya umarci kwamishinoni da AIG na shiyoyi da su sanya ido kan ma’aikatansu.

Wannan umarnin da kwamishinan ya bada ya biyo bayan watanni biyu da kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas ya bada umarnin irin haka a jihar.

Rundunar ta bada wannan umarnin ne bayan korafin da mutane suka yi na yadda jami’an tsaro ke yi musu kutse a cikin wayoyin su da karfin tsiya.

People are also reading