'Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Babban Jami'in 'Yan Sanda a Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu da ake zargin ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe wani babban jami'in ƴan sanda a yankin Arewacin jihar Borno.
Ƴan ta'addan na ISWAP sun kutsa cikin Sabuwar Marte da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Litinin inda suka far wa wani ma’aikacin lafiya wanda ya yi sa’a ya tsere.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ma’aikacin lafiyar ya garzaya ofishin ƴan sanda domin sanar da su halin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ta'addan ISWAP sun hallaka DPO
Lokacin da ya samu kiran gaggawar, DPO ɗin ya bi sawun ƴan ta’addan, amma abin takaici sai suka yi wa tawagar ƴan sandan kwanton ɓauna, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Wani majiyar tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa:
"A jiya ne ƴan Boko Haram suka shiga sabuwar Marte inda suka kashe DPO tare da raunata wasu mutum biyu."
Wani majiya wanda ɗan banga ne ya bayyana cewa:
"Wallahi abin takaici ne. Kwanaki mun rage masa hanya lokacin da muke dawowa daga Dikwa. Ya ce zai je ya ga iyalansa a Maiduguri."
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, Nahum Daso kan mummunan lamarin da ya faru.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa tabbas lamarin hallaka DPO ɗin ya faru.
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane uku ne suka rasa ransu a wasu tagwayen hare-hare da mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta SWAP suka kai a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Hakazalika wasu ƴan banga biyu sun rasa ransu samakon tashin abin fashewa a wani samame da dakarun soji suka kai yankin Kudancin Damboa.
Asali: Legit.ng