Home Back

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 192 sun kama wasu 341 a cikin makon jiya a Najeriya – Hedikwatar Tsaro

premiumtimesng.com 2024/5/10
KISAN GILLAR SOJOJI 17 A DELTA: Yadda aka guntule kawunan soja 14, aka farke cikin su aka fizge zuciyar su

Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta ce a cikin makon daya gabata dakaru sun kashe ‘yan ta’adda 192, sun kamo wasu 341 sannan sun ceto mutum 62 da aka yi garkuwa da su.

Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.

Sannan kuma ‘yan kungiyar ISWAP/JAS 122 da iyalen su sun mika wuya a tsakanin wannan lokaci.

Buba ya ce dakarun sun kwato bindigogi 211 da harsasai 6,288 a cikin wannan mako.

Bayan haka Buba ya ce a Arewa maso Gabas rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan ta’adda of 71 sun kama wasu 143 sannan sun ceto mutum 58 da aka yi garkuwa da su.

Rundunar sojin sama ta yi wa maboyar mahara ISWAP/JAS ruwan bama-bamai a kauyen Kolleram dake kusa da Tafkin Chadi.

Ya ce a wannan harin kadai dakarun sun yi nasarar kashe mahara 30 inda a cikin su akwai manyan kwamandoji kamar su Ali Dawud, Bakura Fallujah da Mallam Ari.

Buba ya ce a Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven da Whirl Stroke’ sun kashe ‘yan ta’adda 29 sun kama 53 sannan sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su.

A Arewa maso Yamma rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe mahara 62, sun kama mutum 49, sun ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun kama mahara 14 tare da makamai da dama da rigunan sojoji.

Sauran kayan da dakarun suka kama sun hada da kullin ganyen wiwi 620, tutar kungiyarfafutukar kafa kasar yarbawa 10, wayoyin hannu 8, kananan radiyo 4 da sauran su.

People are also reading