Home Back

Ƙungiyar Sudawa Alheri, ta baiwa mabuƙata 150 tallafin kuɗaɗe dan rage musu matsin Rayuwa a Kano

dalafmkano.com 2024/5/2

An shawarci al’umma musammam ma mawadata da ƴan kungiyoyin ci gaban al’umma, da su ninka ƙoƙarin su wajan tallafawa mabukata, domin sanya mu su farin ciki a wannan wata na Ramadan da ma sauran watanni.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban kungiyar ci gaban unguwar Sudawa da kewayenta, ta Sudawa Alheri Development Association, Alhaji Aminu Bature, lokacin da suke raba tallafin kudi, ga iyayen marayu da masu karamin karfi a yankin, domin rage musu wani raɗaɗin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Aminu Bature, ya kuma ce ta irin tallafawar ne kowa ke zama cikin farin ciki, musamman ma a tsakanin masu hali da kuma mara shi.

A nasa jawabin ma’ajin kungiyar Nura Ibrahim Karofin Sudawa, cewa ya yi sun ɗauki gaɓarar tallafawa mabuƙatan ne, domin ragewa al’umma radadin halin matsin rayuwar da ake fama da shi, a kasar nan.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa aƙalla mutane ɗari da hamsin kungiyar ta tallafawa da Naira dubu biyar-biyar a ranar Laraba.

People are also reading