Home Back

Gwamna Ya Bai Wa Ƴan Bautar Kasa NYSC Kyautar N200,000 Kowanne, Ya Ɗauki Wasu Aiki

legit.ng 3 days ago
  • Gwamna Umar Bago ya gwangwaje matasan da aka tura Neja aikin bautar ƙasa (NYSC) da abubuwan alheri a wurin rantsar da su
  • Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki malaman lafiya daga cikinsu aiki, sannan za ta turawa kowa kyautar N200,000
  • Bugu da ƙari gwamnan ya bayar da gudummuwat N5bn domin karisa ginin sansanin NYSC da ke ƙaramar hukumar Paikoro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ɗauki matasa masu yiwa ƙasa hidima aiki, waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin kiwon lafiya.

Umaru Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ɗauke su aiki ne domin kawo ƙarshen mutuwar likitoci da sauran malaman lafiya a Asibitocin jihar Neja.

Gwamna Umar Bago.
Gwamnatin Neja ta sanar da ɗaukar dukkan malaman lafiya daga cikin matasa ƴan bautar kasa na jihar Hoto: Mohammed Umaru Bago Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a wurin rantsar da matasa 1,600 da aka tura jihar a rukunin B kashi na 1 2024 a sansanin horar da ƴan bautar ƙasa NYSC da ke Paiko, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wurin rantsar da ƴan bautar kasa, gwamnan ya ce:

"Muna da tsarin ɗaukar aiki kai tsyae ga matasa ƴan bautar ƙasa waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin lafiya, saboda haka idan ka san fannin lafiya ka karanta, gwamnatin Neja ta ɗauke ka aiki kai tsaye."

Ya kuma sanar da bayar da gudunmuwar Naira biliyan 5 don kammala aikin gina sansanin NYSC na dindindin a garin Paiko, hedkwatar ƙaramar hukumar Paikoro.

Har ila yau Gwamna Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa z ata bai wa dukkan matasa 1,600 ds aka turo jihar domin su yiwa ƙasa hidima alawus ɗin N200,000.

"Ina muku maraba zuwa jihar Neja, mu manoma ne, kamar yadda na saba faɗa a ko ina, ina mamakin yadda matashi zai gama jami'a ko kwalejin fasaha amma ya tsaya jiran aikin albashin N60,000.
"Mu a nan jihar Neja a abinci kaɗai ina kashe N500,000 duk wata. Duk wanda aka turo jihar Neja zamu ba shi kyautar N200,000 daga gonakin Neja. Na fahimci ku 1,600 ne, kowanen ku zai ji alat na N200,000."

Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karɓi rayuwar uwargidar mataimakin gwamnan jihar Niger, Hajiya Zainab Garba.

Gwamnan jihar Niger, Alhaji Mohammed Umaru Bago ne ya sanar da hakan a yau Talata a cikin sakon ta'aziyyar da ya fitar.

Asali: Legit.ng

People are also reading