Home Back

Ana Tunanin Zai Karya Farashin Fetur, Ɗangote Ya Fara Wani Muhimmin Aiki a Matatar Mai

legit.ng 2024/7/6
  • Alhaaji Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na ƙara ywan man fetur din da matatarsa za ta riƙa tacewa da ajiye zuwa lita 5.3bn
  • A halin yanzu dai matatar Ɗangote na iya ajiye lita 4.78, amma attajirin ɗan kasuwar ya ce kamfanonin duniya su sayar masa da ɗanyen mai
  • Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote ya yi bayanin yadda ya karya farashin dizal daga N1,700 zuwa N1,000 a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya fara shirin faɗaɗa ƙarfin matatar man fetur ɗin da ya ya gina da ƙarin lita miliyan 600.

Idan hakan ta tabbata a cewar hamshaƙin ɗan kasuwar, matatar za ta riƙa ajiye litar mai 5.3bn.

Alhaji Aliko Ɗangote.
Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na kara girman matatar man da ya gina a Najeriya Hoto: Ɗangote Group Asali: Getty Images

Matatar mai ta Dangote a halin yanzu tana iya ɗaukar lita biliyan 4.78 na man da aka tace, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attajirin ɗan kasuwar ɗan asalin jihar Kano ya yi zargin cewa kamfanonin mai na duniya sun ki sayar masa da ɗanyen msi ​​saboda ba sa son ya ci gaba.

Da aka tambaye shi ko matatarsa ​​za ta karya farashin man fetur wanda a halin yanzu ake sayarwa kan N700 kowace lita, Dangote bai bayar da amsa kai tsaye ba.

Amma attajirin ya yi saurin tunatar da yadda farashin dizal ya fadi daga 1,700 zuwa Naira 1,200 a lokacin da matatarsa ta fara bayar da shi ga ƴan kasuwa.

"Batun man fetur wani abu ne na daban da ke hannun gwamnati. Amma a misali idan kuka kalli dizal, wanda masana'antu da ababen sufuri ke amfani da shi, lokacin da muka fara yana N1,700.
"A mako biyu da shigar namu kasuwa farashim ya karye zuwa N1,000, mun rage kusan kaso 6 cikin ɗari na farashin man dizal. Duk da Dala ta tashi zuwa N1,500 har yanzu dizan na ƙasa da N1,200 a kowace lita.

- Aliko Ɗangote.

APC ta samu ƙarin goyon baya

A wani rahoton na daban mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige, Philip Shaibu da tsohon ɗan majalisar tarayya sun koma bayan jam'iyyar APC.

Manyan jiga-jigan biyu sun bayar da gudummuwa mai tsoka ga kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar APC, Monday Okpebolo.

Asali: Legit.ng

People are also reading