Home Back

Kocin Netherlands ya caccaki VAR kan wasansu da Ingila

bbc.com 2024/8/25
VAR

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Netherlands Ronald Koeman ya soki yadda ake amfani da alƙalan wasa na bidiyo (VAR) bayan da aka bai wa Ingila bugun fanareti a wasansu na daf da na ƙarshe a gasar Euro 2024 a ranar Laraba.

Netherlands ta fara cin ƙwallo ta hannun Xavi Simons, amma tawagar Gareth Southgate ta farke da bugun fenariti a lokacin da Harry Kane suka yi karo da Denzel Dumfries a cikin da'ira na 18

Koeman ya ce: 'A ra'ayina bai kamata ya zama fanareti ba.'

'Ya buga ƙwallon sai kafafunsu suka haɗu, ina ganin VAR na hana mu buga ƙwallo yadda ya kamata, hakika tana daƙile daɗin ƙwallon ƙafa."

Tsohon ɗan wasan baya na Ingila kuma mai sharhi kan ƙwallon ƙafa Gary Neville ya bayyan cewa Netherlands na da babban dalilin jin bacin rai.

'A matsayina naɗan wasan baya, ina ganin hukuncin da aak yanke abin kunya ne,' in ji shi.

'Ba yadda za a yi ya zama fanareti, Ya je ne da niyyar tare ƙwallon, a ra'ayi na ba fanareti ba ne.'

Tsohon ɗan wasan Ingila Alan Shearer ya shaidawa BBC cewa: 'Babu shakka sun taɓa juna, amma mai tsaron baya [Dumfries] yana ƙoƙarin tare ƙwallon ne. ina ganin bai kamata VAR ta yanke wannan hukuncin ba.'

Da wannan rashin nasara ta yi Netherlands ta rasa samun damar lashe gasar a karon farko tun bayan da ta yi nasara a 1988.

People are also reading