Home Back

Bayan Hana Zanga Zanga, Malamai Sun Fara Maganar Ganin Tinubu Domin Samun Mafita

legit.ng 2024/8/25
  • Tattaunawa a kafafen sada zumunta kan shirin fita zanga zanga na cigaba da ɗaukan hankalin al'ummar Najeriya
  • A ranar Jumu'a da ta gabata malamai da dama sun bayyana haramcin fita zanga zanga saboda fitinar da ake tsoro cikinsa
  • Sai dai wasu daga cikin malamai sun fara yunkurin ganin an gana da shugaban kasa kan magance matsalolin tsadar rayuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigerian - Al'ummar Najeriya na cigaba da tattaunawa domin neman mafita kan tsadar rayuwa wanda hakan ke shirin haifar da zanga zanga.

Malamai da dama sun yi hudubobin Jumu'a kan bai halasta a fita zanga zanga ba saboda zai iya kai wa ga tashin hankali.

Sheikh Daurawa
Malamai sun yi kira a zauna da Bola Tinubu bayan hana zanga zanga. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa| Dr. Jamilu Yusuf Zarewa Asali: Facebook

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa a Facebook cewa ya kamata malamai da suka hana zanga zanga su dauki matakin kawo ƙarshen tsadar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurawa: 'Ku zauna da Bola Tinubu'

Shugaban hukumar Hisbah a jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bukaci malaman da suka hana zanga zanga da su zauna da jagororin Najeriya domin neman mafita.

Sheikh Daurawa ya ce akwai bukatar su zauna da shugaba Bola Tinubu, gwamnoni, shugabannin majalisa da sauransu domin magance matsalolin da za su haifar da zanga zangar.

Ya ce kamar yadda malamai suka saka baki kan rikicin Nijar da Najeriya, ya kamata su dauki irin matakin a halin yanzu.

Sheikh Zarewa ya yi kira ga malamai

Babban malamin fikihu kuma mai koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello, Dakta Jamilu Yusuf Zarewa ya yi kira mai kama da na Sheikh Daurawa.

Dakta Zarewa ya ce akwai bukatar a isar wa shugaban kasa halin tsanani da al'umma ke ciki wanda shi ne ke shirin jawo zanga zanga.

Malamin ya wallafa bayanin ne a shafinsa na Facebook yayin da aka masa tambaya kan hukuncin zanga zanga a Musulunci.

Fada da malamai: Albani ya yi martani

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Adam Muhammad ya yi martani ga masu shirin kifar da malamai a kan mimbari saboda hana zanga zanga.

Babban malamin ya bayyana irin shirin da zai rika yi a gida kafin fitowa huɗubar Jumu'a domin tunkarar tsageru da za su kai masa hari a kan mimbari.

Asali: Legit.ng

People are also reading