Home Back

Jami’ar MAAUN dake Nijar ta cira Tuta, ta zama jami’a mai zaman kanta da ke gaba da sauran jami’o’i a Nijar

premiumtimesng.com 2024/5/17
Jami’ar MAAUN dake Nijar ta cira Tuta, ta zama jami’a mai zaman kanta da ke gaba da sauran jami’o’i a Nijar

A bisa ga alkalummar kididdiga da cibiyar AD Scientific Index ta buga, Jami’ar MAAUN, dake Nijar ce jami’ar da ta fi fice da shahara a cikin jami’o’i masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar.

Bisa ga sakamakon gwajin da aka gudanar karkashin hukumar kula da jami’o’i na kasar Nijar wanda aka buga, AD Scientific Index ta ce Jami’ar MAAUN ce jami’a mafi nagarta cikin duka jami’o’i masu zaman kansu a faɗin kasar.

Cibiyar AD scientific Index ta ce ta yi amfani da gwaji kan fasahar kimiya da kuma kwarewa a harkar karantarwa da kuma nazarin kimiya a fannonin karatu na jami’ar.

Sakamakon gwajin ya nuna kaf gabaɗaya jami’ar MAAUN ɗin ta yi wa sauran jami’o’i masu zaman kansu zarra.

Jami’ar MAAUN dake Nijar, ita ce jami’a ta farko da aka kafa a Nijar dake karatu da harsunan turanci da kuma Faransanci.

Jami’ar ta yaye ɗalibai da dama a darussa da daban daban.

Shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Gwarzo ya yaba da wannan karamci da AD scientific Index suka yi wa jami’ar yana mai cewa jami’ar za ta cigaba ba ba mara ɗa kunya wajen inganta fannoni da sassan darussan da ake koyarwa a jami’ar.

People are also reading