Home Back

Za a ɗauki shekaru kafin kwance bamabaman da ba su fashe ba a Gaza - MDD

bbc.com 2024/5/5

Asalin hoton, Getty Images

Ɓaraguzan gidajensu kawai Falasɗinawa suka tarar a yankin Khan Younis bayan wata shida Isra'ila na luguden wuta a yankin
Bayanan hoto, Ɓaraguzan gidajensu kawai Falasɗinawa suka tarar a yankin Khan Younis bayan wata shida Isra'ila na luguden wuta a yankin
  • Marubuci, Nirvana Elsaied
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic Trending
  • Mintuna 8 da suka wuce

Hotunan wuraren da Isra'ila ta ragargaza kudancin Gaza sun karaɗe duniya ta intanet tun bayan da ta janye akasarin sojojinta daga yankin Khan Younis a farkon watan Afrilu.

Yayin da Falasɗinawan da aka kora ke komawa gidajensu don ganin abin da ya rage, wata sabuwar matsala kuma ta kunno kai - ita ce bamabaman da ba su fashe ba.

Ofishin ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya mai suna UNOCHA ya gudanar da bincike a Khan Younis 'yan kwanaki bayan haka.

"Tituna da sauran walwalar jama'a na cike da ababen fashewar da ba su kai ga fashewar ba, abin da ke barazana ga fararen hula," kamar yadda ya bayyana cikin wata sanarwa.

"Tawagar ta gano bamabamai masu nauyin kilogiram 450 da ba su fashe ba a kan hanyoyi da kuma cikin makarantu."

Ƙwararru kan harkokin soji sun yi hasashen cewa dakarun sojin Isra'ila sun jefa dubban bamabamai tun daga fara wannan yaƙi.

Asalin hoton, UNOCHA/Themba Linden

Wata tawagar MDD ta gano bamabamai masu nauyin kilogiram 450 a kan hanyoyin Khan Younis ranar 10 ga watan Afrilu
Bayanan hoto, Wata tawagar MDD ta gano bamabamai masu nauyin kilogiram 450 a kan hanyoyin Khan Younis ranar 10 ga watan Afrilu

MDD na da tawaga ta musamman a Gaza da ke ganowa da kuma kwashe bamabaman da ba su fashe ba mai suna UN Mine Action Service (UNMAS).

Charles (Mungo) Birch ne shugaban tawagar ta MDD kuma ya ce ɓaraguzan da ke Gaza sun zarta na Ukraine.

"Akwai ababen fashewa iri-iri kamar waɗanda ake harbowa daga jirgi da kuma ƙananan makaman roka."

Mista Birch ya ce sun yi ƙiyasin cewa kashi 10 cikin 100 na makaman sun kasa yin aiki ne.

Ya kuma ce Isra'ila ta yi amfani da jirage wajen harba bamabaman kan hanyoyin da ke ƙarƙalshin ƙasa.

Kafin harin da Hamas ta kai a Isra'ila, UNMAS ta kusa kammala kwashe manyan bamabamai 21 da aka harba da jiragen sama daga Gaza, waɗanda ɓurɓushin rikice-rikice ne tsakanin Isra'ila da Hamas da suka gwabza a baya.

Sai da aka shafe wata ɗaya ana ƙoƙarin kwance kowane bam ɗaya, amma kwatsam sai abubuwa suka sauya.

Harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba ya kashe mutum aƙalla 1,200 tare da yin garkuwa da wasu sama da 250 zuwa cikin Gaza.

Nan take Isra'ila ta mayar da martani.

Ministan tsaro Yoav Galant ya ce Isra'ila ta harba bam da makamai masu linzami 10,000 a kan Zirin Gaza cikin kwana 26 na farkon yaƙin.

"Lamari ne mai ƙamarin gaske," in ji Mista Birch.

A ƙarshen watan Maris, duk da kiraye-kirayen da ƙungiyoyin kare haƙƙi da wasu 'yan jam'iyyar Democrat ta Shugaban Amurka Biden suka dinga yi, jaridar Washington Post da Reuters sun ruwaito cewa Amurkar ta amince da bai wa Isra'ila bamabamai sama da 1,000 nau'in MK84 2,000lb da kuma 500 nau'in MK82 500lb.

An ruwaito cewa irin waɗannan bama-baman ne aka yi amfani da su wajen kai munanan hare-hare kan mutanen Gaza.

Aƙalla mutum 33,970 Isra'ila ta kashe a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza ƙarƙashin ikon Hamas.

Hare-haren ragargaza Gaza

Rundunar sojin Isra'ila ko kuma IDF ba ta taɓa bayyana nau'in makaman da take amfani da su ba wajen kai hare-hare. Amma ana iya cewa hotunan makaman da ake gani tana sakawa a shafukanta na zumunta su ne take amfani da su a yaƙin da take yi a Gaza.

Masanin makamai a ƙungiyar Amnesty International, Brian Castner, ya ce Isra'ila ta jefa bamabamai marasa linzami MK84 2,000lb (masu nauyin 900kg) saboda irin ɓarnar da ake gani a Gaza.

"Matsalar bamabaman MK84 ita ce suna da girma da kuma nauyin 900kg, waɗnda rabinsu abubuwan fashewa ne sauran kuma ƙarfe, kuma za su iya raunata fararen hula daga nesa," a cewarsa.

"Saboda haka, dole ne a kai su wani wurin don lalata su cikin kwanciyar hankali. Zirin Gaza ƙaramin wuri ne saboda haka abin zai yi wuya sosai a can."

Ya ƙara da cewa barin bamabaman da ba su fashe ba a ƙarƙashin ɓaraguzai kuma a wuri mai cunkoso abu ne mai haɗari.

Sashen BBC Arabic Trending ya tambayi sojin Isra'ila game da wuraren da suka kwashe bamabamai a Gazan.

"Ku yi haƙuri, ba za mu iya bayyana muku takamaiman wurare ba," in ji wani mai magana da yawun rundunar.

Asalin hoton, Getty Images

Ana gudanar jana'iza a kullum a Zirin Gaza saboda hare-haren Isra'ila
Bayanan hoto, Ana gudanar jana'iza a kullum a Zirin Gaza saboda hare-haren Isra'ila

Mista Castner ya ce akwai makaman roka da Hamas ke harbawa waɗanda su ma ke da haɗari idan aka bar su ba tare da kwashe su ba.

Ya kuma bayyana yiwuwar Hamas za ta iya farfaɗo da wasu bamabaman na Isra'ila da ba su fashe ba.

Asalin hoton, Getty Images

Wasu yara sun sama wa kan su filin wasa a cikin ɓaraguzai amma kuma akwai yiwuwar samun bamabaman da ba su fashe ba a cikinsu
Bayanan hoto, Wasu yara sun sama wa kan su filin wasa a cikin ɓaraguzai amma kuma akwai yiwuwar samun bamabaman da ba su fashe ba a cikinsu
People are also reading