Home Back

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayar da Tallafin N50,000 Ga Mutanen Najeriya

legit.ng 2024/5/17
  • Gwamatin tarayya ta sanar da cewa ta fara raba tallafin kudi na 'shirin bayar da tallafi mai dauke da sharadi na shugaban kasa (PCGS)'
  • Ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, Doris Aniete ta bayyana hakan a ranar Talata, inda ta ce tuni aka fara tura kudin
  • Aniete ta kara da cewa zuwa ranar Juma'a, 19 ga Afrilu za a sake biyan kudin amma ba duka wadanda suka nemi tallafin ne za a biya yanzu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari ta ce ta fara raba tallafin kudi na shirin PCGS ga 'yan Najeriya.

Shirin PCGS wani tallafi ne da yake karkashin shugaban kasa wanda aka warewa N200bn domin bayar da rance mai sauki ga kananan 'yan kasuwa da masu sana'a.

Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin kudi ga 'yan Najeriya
Gwamnati ta ce ba duka wadanda suka nemi tallafin ne za su samu kudin a yanzu ba. Hoto: @officialABAT, @DrDorisAnite Asali: Twitter

Yaushe za a sake biyan kudin?

Gwamnati ta hannun bankin masana'antu ta ce za ta raba N200bn din ne a matakai guda uku da kuma dukkanin wadanda suka cancanta za su samu kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Doris Aniete, ministar kasuwanci ta wallafa wani rahoto a shafinta na Twitter a ranar Talata tana mai cewa tunin wasu daga cikin wadanda za su gajiyar tallafin suka sami kudadensu.

Aniete ta kara da cewa zuwa ranar Juma'a, 19 ga Afrilu, za a sake biyan kudin ga wani adadi mai yawa na wadanda aka tantance.

Kowa ne zai samu tallafin yanzu?

Ta ce:

"An fara bayar da kuɗin 'shirin bayar da tallafi mai dauke da sharadi na shugaban kasa'. Ana ci gaba da tsare-tsare kuma tuni wasu masu cin gajiyar tallafin sun sami kudinsu.
"Yana da mahimmanci a fahimci cewa ana ci gaba da biyan kuɗin ne yanzu, kuma ba duk masu neman tallafin ba ne za su sami kudin a wannan rabon na farko."

Duk da hakan, ministar ta bayar da tabbatacin cewa duk masu neman tallafin da aka tantance za su sami kudin su a matakai na gaba

Asali: Legit.ng

People are also reading