Home Back

Gasar Hikayata ta Mata Zalla ta BBC Hausa 2024

bbc.com 2024/7/7
Logo

Hikayata gasa ce ta rubutun ƙagaggun gajerun labarai ta mata zalla wadda ke samar da dama ga mata zalla marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa.

Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.

Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa.

Gasar dai ta mata zalla ce waɗanda shekarunsu ba su gaza 18 ba sannan kuma ba su wuce 35 ba ya zuwa ranar 24 ga watan Agustan 2024.

Za a rufe gasar ne da ƙarfe 11:59 agogon GMT na ranar 24 ga watan Agustan 2024. Ba za a yi maraba da duk labarin da aka aiko bayan rufe gasar ba.

Akwai tukwicin kuɗi da lambar karramawa da za a bai wa gwarazan gasar.

Yadda za ku shiga gasar

Ku karanta cikakkun bayanan na Ƙa'idodjin da dokokin gasar da na Bayanan Sirri na BBC.

Dole ne a aiko da labaran ta ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin biyu:

Ta hanyar cike wannan fom ɗin

Ko kuma

Ta hanyar aikewa da labarin zuwa adireshin imel bayan sauko da cike wannan fom ɗin sai kuma a aika zuwa wannan adireshin namu na imel labari.bbchausa@bbc.co.uk

Ka da a manta cewa dole ne mai shiga gasar ta zama mai shekara tsakanin 18 zuwa 35 sannan kuma wannan gasa ce ta mata zalla.

Za a sanar da waɗanda suka samu nasarar zama gwarazan gasar a yayin wani biki da BBC za ta shirya a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar 28 ga watan Nuwamban 2024. Za a sanar da bayanan a shafin BBC Hausa da rediyo.

Ku nemi karin bayani dangane da gasar a Ƙa'idodjin da dokokin gasar da Bayanan Sirri na BBC.

Tsarin gasar

Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne, bisa jagorancin ma'aikacin BBC za su zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su zaɓi ta biyu da ta uku.

Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu kowane irin bayani kan masu shiga gasar ba.

Tawagar alƙalan za ta zaɓi labarai 30 bayan tantancewa ta farko sannan daga bisani za a sake tantancewa a fitar da guda 15, inda a tantancewa ta uku za a fitar da ta ɗaya da ta biyu da ta uku sai kuma 12 da suka cancanci yabo.

Waɗanda suka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan ɗaya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu ɗari biyar) ga wadda ta zo ta uku.

BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.

Za a sanar da mutum ukun da suka zamo zakaru a yayin wani bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya.

BBC za ta sanar da lokacin bikin ta hanyar wallafa bayanin a shafukanta na intanet da na social midiya.

People are also reading