Home Back

Kotu ta sanya ranar da za ta bayyana matsayar ta kan shari’ar Masarautun Kano

dalafmkano.com 2024/7/4

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Gyaɗi-gyaɗi a nan Kano, ta sanya ranar 13 ga wannan watan dan bayyana ra’ayinta a kan tattaunawar da lauyoyi suka yi a gabanta, a ƙunshin karar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun Kano 4 da majalisar dokokin jihar tayi a baya.

A zaman kotun na lauyan gwamnatin Kano Barista Mahmud Magaji SAN, ya yi suka akan hurumin kotun inda ya kawo wasu misalai na wasu shari’o’in da kotun koli ta yi.

Shima lauyan majilisar dokoki ta jahar Kano Barista Ibrahim Wangida, ya yi suka akan hanyar da mai karar ya bi ya shigar da karar bata da tushe.

Barrister Wangida ya bayyana cewar shi mai kara Aminu Babba ba Ɗan majalisar dokoki ba ne, kuma lokacin da ya shigar da karar an riga an rushe dokar da ta naɗa shi a matsayin sarkin dawaki babba dan haka bashi da hurumin zuwa kotu ta ƙalubalantar abin da majalisar tayi.

Majalisar dokokin jahar Kano dai ta rushe dokar masarautu ta shekarar 2019 wadda ta raba masarautar Kano gida biyar, kuma bayan rushe waccan dokar ne gwamnan Kano ya sanya hannu akan sabuwar dokar, tare da bayyana Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarkin Kano na 16.

Mai kara ya bayyanawa kotun cewar hanyar da majalisar ta bi dan yin sabuwar dokar akwai gyare a cikinta.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, kotun ta kuma sanya ranar 13 ga wannan watan domin bayyana matsayar ta.

People are also reading