Home Back

"Kwankwaso Zai Maka Illa": Buba Galadima Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Shiga Siyasar Kano

legit.ng 2024/6/29
  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, jigon NNPP, Buba Galadima ya gargadi Shugaba Bola Tinubu
  • Galadima ya ja kunnen Tinubu da ya yi hankali da shiga lamarin siyasar Kano ko ya lalata siyasarsa a Najeriya
  • Jigon NNPP ya ce tun farko bai kamata Gwamnatin Tarayya ta nuna goyon bayanta ga bangare guda daya ba a rigimar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan shiga rigimar Kano.

Galadima ya ja hankalin Tinubu kan takalar Rabiu Kwankwaso saboda zai iya jawowa kansa matsala a siyasa.

Jigon NNPP ya bayyana haka a faifan bidiyon YouTube yayin hira da Arise TV a jiya Talata 18 ga watan Yuni.

Ya ce ya kamata Tinubu ya yi hankali da shiga siyasar Kano ko kuma ya lalata damarsa ta shugabancin Najeriya a jihar.

"Gwamnatin Tarayya da Bola Tinubu su yi taka tsan-tsan da siyasar Kano ko kuma ya ruguza siyasarsa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Buba Galadima

Jigon siyasar NNPP ya caccaki Gwamnatin Tarayya kan nuna goyon baya ga bangare daya inda ya ce bai kamata ta shiga lamarin sarauta ba.

Galadima ya yabawa ƴan jihar Kano kan yadda suka doge kan gaskiya duk da dambarwar sarautar jihar da ake ciki.

Kwankwaso ya zargi Tinubu da kawo rudani

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da neman kawo rudani a jihar Kano.

Kwankwaso ya zargi shugaban da shirin sanya dokar ta ɓaci domin samun damar kwace mulkin NNPP daga hannunsu.

Sai dai daga bisani, Tinubu ya yi martani inda ya ke musanta wannan zargi na Kwankwaso da cewa ba shi da tushe.

Asali: Legit.ng

People are also reading