Home Back

NDLEA ta sake kama masu safarar kwayoyi a tashar jiragen Lagos

rfi.fr 2024/5/4
Daya daga cikin mutanen da NDLEA ta kama dauke da kwaya
Daya daga cikin mutanen da NDLEA ta kama dauke da kwaya © NDLEA

Najeriya – Wani 'dan Najeriya ya yi amai da kuma kashin dauri 80 na hodar ibilis da ya hadiye a cikin sa, lokacin da aka kama shi a tashar jiragen saman Lagos yana kan hanyar tafiya kasar India.

Hukumar NDLEA dake yaki da sha da kuma safarar kwayoyin ta kuma kama wani mai safarar kwayar tare da layu a tashar jiragen ruwan Tincan dake Lagos inda ta kwace dauri 2,144 na tabar wiwi da aka shiga da ita kasar daga Colorado.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya shaidawa manema labarai cewar jami'an hukumar a tashar jiragen saman Murtala sun kama Freeman Charles Ogbonna a wurin da ake gudanar da bincike kafin hawa jirgi, inda aka gano ya hadiye dauri 80 na hodar ibilis.

Freeman Charles Ogbonna da NDLEA tace ya yi amai da kashin dauri 80 na hodar ibilis
Freeman Charles Ogbonna da NDLEA tace ya yi amai da kashin dauri 80 na hodar ibilis © NDLEA

Babafemi ya ce an kama Ogbonna wanda yake dauke da fasfo na kasar Liberia ne a ranar 31 ga watan Maris lokacin da yake kokarin hawa jirgin Qatar Airways dauke da sunan Carr Bismark, yayin da bincike ya gano cikakken sunan sa na 'dan Najeriya Freeman Charles Ogbonna.

Bayan tsare shi a dakin bincike na hukumar, Ogbonna ya yi amai da kuma kashin dauri 80 na hodar da ya hadiye a cikin sa.

Daga bisani wanda ake zargin ya shaidawa NDLEA cewar wani 'dan uwansa ne ya sanya shi cikin wannan mummunan aikin na hadiye gram 889 na hodar domin safarar ta, yayin da aka masa tayin biyan shi naira dubu 300.

Babafemi yace har ila yau, jami'an NDLEA sun kama Imran Taofeek Olalekan dauke da kwaya lokacin da yake kokarin hawa jirgi a tashar Murtala Muhammed zuwa kasar Oman.

Wasiu Jimoh da NDLEA ta kama da kwaya
Wasiu Jimoh da NDLEA ta kama da kwaya © NDLEA

Jami'in yace Imran ya boye kwayar ce a karkashin jakarsa, kuma take aka kama shi da wanda ya raka shi tashar jiragen da aka bayyana sunan sa a matsayin Ishola Isiaka Olalekan, wanda ya yi hayar sa domin safarar kwayar.

Olalekan yace an masa tayin naira miliyan guda da rabi ne domin kai kwayar, yayin da wanda ya dauke shi kuma za'a biya shi naira dubu 200.

Babafemi yace an gano wasu layu da mutanen biyu suka yi amfani da su wajen ganin sun kaucewa jami'an hukumar.

A wani labari kuma, NDLEA ta kama dauri 2,144 na tabar wiwi da nauyin sa ya kai kilo 1,072 a tashar ruwan Tincan da aka shiga da shi kasar daga Colorado.

People are also reading